Tuesday, December 25, 2007

Lalacewar ’Yan Nijeriya Ta Kai Inda Ta Kai Ne?



Kwanan baya na hau bas daga wata unguwa a cikin garin Abuja zuwa inda ofishin da nake aiki yake. Kafin in hau sai da kwandastan (conductor) bas d'in ya shaida mini kud'in da zan biya, na kuma amince.
Lokacin da muka iso Kasuwar Wuse, fiye da rabin fasinjojin bas d'in suka sauka, kwandasta ya d'ebi wasu sabbi. Kasancewar nisan Kasuwar Wuse da inda zan sauka kusan rabin tafiyar daga inda na hau ne, babu mamaki idan kudi'n motar sabbin fasinjojin ya kasance rabin nawa.
Ba a jima da fara tafiya ba, sai kwandsta ya nemi mu biya kud'in mota. Na d'auko kud'i na bashi. Abin da na bayar daidai abin da ya shaida mini ne tun da farko. Amma sai kwandastan ya yi zaton daga Wuse na hau, don haka ya 'kirgo canji ya bani. Ni kuwa sai na mayar masa da canjinsa na ce “ai ba daga Wuse na hawo ba”.
Ganin haka sai fasinjan da ke kusa da ni ya yi mamaki, ya ce “lallai kai d'an 'kasa ne na gari”. Amma ni ban ga wani abin mamaki ba a wannan al’amari.
Bayan an kwana biyu sai na sake hawa mota—wannan karon tasi—daga kusa da gidan da nake zaune zuwa wajen aiki na. Lokacin da na iso tashar da zan hau mota sai na samu motar da ke lodi ba kowa, don haka na samu damar hawa gaba. Wata 'kila saboda yawan 'karin kud'in mai da aka yi ta yi direboda suka yi ta 'korafin cewa ba su samu su mayar da kud'in jigila balle su samu riba, ba ba'kon abu bane a Nijeriya ka ga an d'auki fasinja biyu a gaba, hud'u a baya. A Abuja, saboda sa-idon da jami’an Hukumar Kare Had'urra ta 'Kasa (Federal Road Safety Commission [FRSC]) ke yi musamman wajen ganin an yi amfani da d'amarar kujera (seat belt), a kan d'auki mutum d'aya ne a gaba, hud'u a baya.
Ina zaune a mota har ta kusan cika, saura mutum d'aya. Can sai ga mutum d'aya ya zo, amma fa yana da 'kiba sosai, don haka sauran wajen da ya saura a bayan mota ya yi masa kad'an. Nan aka fara sa'ke-sa'ken yadda za a yi. Wasu su ka bayar da shawarar cewa ya jira motar da za ta yi lodi ta gaba, shi kuma ya ce tun da ya yi sa’a ya samu mai tafiya nan take baya sha’awar zama jiran sai wata motar ta cika.
Nan fa direban motar ya zo ya same ni a kan in yi ha'kuri in koma baya, in ya so wannan mutumin mai 'kiba ya hau gaba. Ganin akwai hikima a yin hakan—tun da ni ba wata 'kiba ba ce da ni—sai na sauka na koma baya ba tare da na yi musu ba. Hakan ya janyo mini yabo daga fasinjojin motar, wad'anda suka ce lallai ni d'an 'kasa ne na gari.
Wad'annan abubuwa biyu da suka faru suka sanya na fara tunanin cewa "shin lalacewar 'yan Nijeriya ta yi matu'kar tsanani ne da har in mutum ya aikata gaskiya ko ya yi taimako za a ri'ka yabonsa haka?" Ni a ganina dukkan addinan da 'yan Nijeriya suke yi sun yi horo da aikata gaskiya, da kuma taimakon juna. A sanina ga Musulmi Al-'Kur’ani ya yi horo ba kawai a aikata gaskiya ba, a ma kasance da masu gaskiya. Sannan kuma tarihi ya nuna cewa taimakon da Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi) ya yi wa wata tsohuwa shi ya sanya ta ta musulunta duk da ta kasance mai 'kin sa (shi Manzon).
Haka ma abin yake a addinin Kirista, inda Littafin Baibul ya ce ri'kon gaskiya na sanya al’umma ta d'aukaka. Sannan kuma ya ce, a wani wuri na daban, ka kasance mai tallafawa d'an-uwanka. Kai ko mutum ba ya yin addini, wad'anda babu ruwansu da addini suna nuni da cewa su masu 'kaunar d'an-Adam ne don haka a ko yaushe a shirye suke su taimaki mutane. Amma ga alama 'yan Nijeriya sun manta da duk wannan.
Baya ga addini, babu mamaki kasancewa ta d'an arewa ya taimaka wajen ganin cewa abin da na yi ba wani abin a-zo-a-gani ba ne. A ma'kalar da ya ke rubutawa duk mako a jaridar Weekly Trust, Segun Odegbami ya ta'ba cewa zaman da ya yi da 'yan arewa ya gane cewa su mutane ne masu tsantseni, da wadatar zuci, da kuma rashin had'ama. Idan dai aka je aka zo, za a dawo kan maganar addini domin wad'annan halaye na 'yan arewa ko shakka babu sun samo tushe ne daga tasirin da addini (musamman Musulunci) ya yi a rayuwarsu. Addini ya sa mutumin arewa ba shi da wuyar rungumar 'kaddara. Sau da yawa za ka ga wasu sun tafka asara wadda a sanadiyyar ta sun suma ko ma sun she'ka barzahu, amma d'an arewa idan ya tafka irinta sai ka ji ya ce “Haka Allah Ya so”, ya ci gaba da harkokinsa. Ko da zai yi ba'kin ciki, zuwa wani lokaci sai ya manta.
Ga wanda ya san al'adar Malam Bahashe, misali, ya san cewa idan aka yi mutuwa ya kan je ya yi gaisuwa. Gaisuwar kuma ba ta wuce: “Ya (aka ji da) ha’kuri?” ba. Martanin da wanda aka yiwa rasuwar yake mayarwa shine: “Ha'kuri ya zama dole” ko kuma “Ha'kuri sai Ma’aiki (Manzon Allah)”. Abin nufi shine: “Manzo ya karantar da mu mu yi ha'kuri da duk abin da Allah Ya d'ora mana”.
Kwanan nan kafofin yad'a labarai suka ruwaito labarin wani mutum da ya tsinci kud'in da suka kai kimanin miliyan tamanin na nairori (N80,000,000), da kuma wata 'yar 'Kato-Da-Gora (Nigeria Security and Civil Defence Corps) wadda ta tsinci dubban nairori a mota, amma suka nemi masu kud'ad'en don su mayar masu da abinsu. Nan take na tuna kwana bakwai kacal kafin faruwar haka na shaida zage-zage da aka yi tsakanin direban tasi da fasinjansa a kan naira goma (N10.00) kacal. A 'ka’idar 'yan tasi akwai kud'in da za a biya zuwa ko wanne wuri. Kuma ana amfani da sunan wurin tsayawar bas (bus stop) na bakin titi a wurin. Ke nan ana wuce wurin tsayawa, kud'i ya 'karu. A haka ne shi wannan fasinja za shi wani wuri, in an wuce inda ya fad'a, amma nisan bai fi taku d'ari biyu ba daga wurin tsayawa na baya. Lokacin da aka iso wurin tsayawar da fasinja ya ambata sai direba ya ja birki; shi kuma fasinja ya ce ba a zo inda zai sauka ba. Direba ya ce muddin ya 'ketare wannan wuri sai fasinja ya 'kara kud'i har naira goma. Fasinja kuma ya ce shi sam ba zai sauka ba sai an 'karasa da shi, kuma ba zai 'kara ko kwabo ba. Sauran fasinjojin da ke motar suka fara mita a kan ana 'bata masu lokaci, sai direba ya ce in har ya motsa da fasinjan nan ba zai tsaya a inda fasinjan zai sauka ba. Ya kuwa fizgi mota zai yi gaba. Isowa inda zai sauka ke da wuya, sai fasinja—dama a gaba ya ke kusa da direba—ya yi wuf ya ri'ke sitiyari, mota ta fara tangal-tangal. Nan fa aka tsaya ana ta cacar baki, har aka kusa a ba hammata iska—duk a kan naira goma. Wannan ke nan: son banza, da rashin wadatar zuci, da rashin ha'kuri, da ma son cuta abubuwa ne da suka zama ruwan dare a tsakanin 'yan Nijeriya.
Ga kuma talauci da ya yi wa al'ummar 'kasar 'kofar rago. Mutum ba zai fahimci irin 'kuncin rayuwa da 'yan Nijeriya ke fama da shi ba sai ya je wasu unguwanni a gefen birnin Abuja. Duk da rusau d'in da el-Rufa’i ya yi kusan shekaru hud'u ya na yi a Abuja akwai wuraren da mutane ke kwana a rumfunan kara wad'anda 'kwa'k'kwarar iska za ta iya d'aukewa. Kai wasu ma a 'kar'kashin gadar fly-over su ke kwana. Ga wanda bai san fly-over ba, ita ce hanyar motar da ta wuce ta saman wata hanyar don ba a son samun cinkoson motoci. Idan ba na manta ba na ta'ba jin wani mtumin yankin Naija Delta yana 'korafin cewa yawan gadar fly-over da ke Abuja ya fi yawan gadojin da suka 'ketare rafuka da 'koramu a yankin wanda daga nan ne Nijerya ta ke samun kaso mafi tsoka na kud'in shigar ta.
Amma fa kar a manta cewa el-Rufa’i ya ce ba don talakawa aka yi Abuja ba.

Friday, December 14, 2007

JASAWA SUN BARA


Lokacin da Jasawa suka yanke shawara su 'ki fitowa aiki ko kasuwa don nun rashin jin dad'insu da abin da suka kira halin ko-in-kula da gwamnatin Jihar Filato take nunawa ga al'amuran da suka shafe su, abin ya baiwa kowa mamaki.
Hasali ma tasirin wannan ho'b'basa ya girgiza Jihar gaba d'aya, kama daga gwamnati har zuwa talakawa. Ba zato ba tsammani kawai aka wayi gari babu kowa a kasuwa babu wanda ya bud'e shago, babu motoci a tituna. A karon farko al'ummar Jasaw suka yanke shawarar d'aukar mataki kuma kowa ya bayar da had'in kai sa'banin yadda abin yake a can baya.
Daga cikin abubuwan da Jasawa suke adawa da su da suka sanya su d'aukar wannan mataki akwai yun'kurin da Gwmanan Jihar, Da David Jinah Jang ya ke yi an tshin sakatariyar 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa daga inda take a yanzu ya mayar da ita ofishin Hukumar Tsabtace Garin Jos (Jos Metropolitan Development Board [JMDB]).
Al'ummar Jasaswa na ganin cewa d'auke sakariyar daga inda take a yanzu a mayar da ita wani waje mataki ne da gwmnatin ke 'ko'karin d'auka don nesanta su da harkar mulki a 'karamar hukumar kwata-kwata. Sanin kowa ne cewa wurin da sakatariyar take a yanzu wuri ne da Jasawa ke tin'kaho da shi a matsayin nasu-ko ba komai su kan ri'ka jin duk wani 'kwa'k'kwaran motsi da aka yi. Amma idan sakatariyar ta bar wajen shi ke nan sai a ri'ka yi babu su.
Dalili na biyu da ya sa Jasawa ba su amince da d'auke sakatariyar ba shi ne shirin da aka ce Gwmna Jang yana yi na gina wata 'kasaitacciyar majami'a a wurin da sakatariyar take. Hujjar Gwamnan ta yin hakan, kamar yadda wasu majiyoyi suka ruwaito, itace cewa a garuruwan sarakunan arewa za ka samu a kusa da fadar sarki akwai masallacin Juma'a. Don haka ya ke ganin ya kamata a ce a kusa da fadar Gbong Gwom (Sarkin Birom) wadda take kusa da sakatariyar akwai katafariyar majami'a.
Sai dai al'ummar gari suna gani rashin dacewar wannan hujja domin a cewarsu Gbong Gwom din nan, tun ma kafin rikicin da yayi kaca-kaca da garin Jos a shekarar 2001, ba ya kwana a wannan fadar. Saboda haka, a ganisu, akamta ya yi a tafi ko ma ina ya ke kwana a gina masa majami'a. Sannan kuma tarihi ya nuna cewa kusa da inda fadar Gbong Gwom d'in take, nan ne asalin fadar Sarkin Jos Isiyaku, wanda yake Bahaushe ne, kafin Turawan mulikin mallaka su kar'be sarautar su baiwa Rwang Pam. Bugu da 'kari kuma Jasawa suna ganin cewa tun da a yanzu 'yan 'kabilar Birom d'in da ke 'karamar hukumar Jos ta Arewa ba su da yawa, kamata yayi a d'auke fadar Gbong Gwom d'in gaba d'ayanta a mayar da ita inda mabiyansa ke da rinjaye.
Ko da yake wannan yajin fita da Jsawa suka yi ya yi matu'kar nasara da tasiri, an samu wasu balgurbi da suka nemi a yi wa al'amarin 'kafar ungulu. Daga cikinsu akawai wani wasu 'yan siyasa da suka shiga gari suna surutai suna sukar shugabannin al'umma. Wad'annan mutane, idan ab su yi a hankali ba, na fuskantar barazanar rasa samun kwanciyar hankali a tsakanin al'umma domin kuwa kowa na yi musu tofin Allah-tsine. A cikinsu akwai wanda aka ba shi wani mu'kami da ke da muhimmanci ga rayuwar ibadar Muslmi. Kuma wata majiya ta ruwaito cewa an bshi wannan mu'kami saboda an san cewa shi lalatacce ne, wanda zai iya had'a baki don cutar da al'ummarsa matu'kar zai samu d'an abin miya.
Hausawa dai na cewa "In rana ta fito tafin hannu bai iya kare ta" sannan kuma "Kowa ya daka rawar wani to tasa za ta 'baci". In kunne ya ji....

Saturday, March 24, 2007

Ina ne Asalin Jasawa?

Ina ne Asalin Jasawa?

Kalmar Jasawa na iya d'aukar ma'anoni guda biyu. Ma'ana ta farko itace ta fuskar sunan al'umma ko mazauna gari; misali, mutanen Kano ana kiran su Kanawa, na Katsina Katsinawa, na Sakkwato Sakkwatawa, da sauransu. Ke nan Jasawa na nufin mutanen Jos, ba tare da an bambance wasu daga wasu ba.

A ma'ana ta biyu, wadda yawanci ita aka fi fassara kalmar da ita, akan ce Jasawa ta samo asali ne daga kalmomi guda biyu: Jos da Hausawa. Ke nan idan aka ce Jasawa ana nufin Hausawan Jos. Ita ma kanta kalmar Jos an yi sa'bani wajen fassara ta. Wasu sun ce kalmar ta samo asali ne daga harshen Birom, wasu kuma sun ce sunan wani bature ne.

Ala ayyi halin, Hausawan Jos Jasawa ne ta ko wacce siga mutum ya fassara wannan kalma. Masana tarihi sun bayyana cewa Hausawa sun kwaranya zuwa wurin da ake kira Jos ne a matakai biyu, ko uku. Matakin farko shine wad'anda ake kira d'iban gwamna.

Lokacin da Turawa suka gano kuza a yankin Tsaunukan Jos (Jos Plateau), sun nemi ma'aikatan da za su yi aikin ha'kar wannan ma'dani, amma ma'aikata sun yi 'karanci. Don haka Turawa suka bu'kaci sarakunan 'kasashen Hausa su samo masu ma'aikata. 'Ko'karin da sarakunan suka yi na rarrashin jama'ar su su yarda su zo wannan aiki ya ci tura; don haka aka kwaso mutane 'karfi-da-yaji aka kawo su.

Kashi na biyu kuma sune 'yan kasuwa, wad'anda su kan kawo kayan biyan bu'kata ga wad'ancan ma'aikatan. Wad'annan 'yan kasuwa su kan tafi 'kasashen Hausa su sayo kaya kama daga kayan abinci zuwa na bu'katun yau da kullum, sannan su kawo su sayar a 'kasar kuza (Jos). Da tafiya tai tafiya sai wasu daga cikin wad'annan 'yan kasuwa suka zama diloli suka share wuri suka zauna - sun ma sun zama 'yan gari ke nan.

Daga nan kuma sai aka samu wani kashin wanda shima na 'yan kasuwa ne. Sai dai su wad'annan ba zuwa suke yi su sayo kaya su zo su sayar ba. Hasali ma su ba mazauna garin ba ne, su kan zo lokacin rani, idan damina ta fad'i kuma sai su koma wuraren da suka fito don yin noma. Wad'annan ake kira 'yan-ci-rani. To suma da tafiya ta yi tafiya wasu daga cikin su Allah Ya yi masu bud'i, sai suka gina gidaje, suka yi aure, suka hayayyafa.

Amma wannan ba yana nufin cewa Hausawa ba su ta'ba zuwa yankin Tsaunukan Jos kafin zuwan Turawa ba ne. Wannan dai shine bayanin yadda Hausawa masu d'imbin yawa suka kwararo suka zauna a yankin.

Da yawa daga cikin mutanen da suka taho Jos daga 'kasashen Hausa ba su zo da niyyar zama ba. Wata'kila ma wannan ne ya sa gidajen da suka gina a wancan lokaci a wuraren da sansanonin ma'aikata suke ba su cika yalwa ba. Misali idan mutum ya shiga unguwar Gangare ko wasu unguwanni makamantan ta zai ga gidajen du-du-du ba su fi a gina d'aki d'aya da falo a wurin ba - amma kuma akwai d'akunan kwana uku ko fiye da na girki, da na wanka ko magewayi.

Kasancewar wad'annan mutane sun taho da niyyar komawa garuruwansu ko-yau-ko-gobe ya sa wasu daga cikin su ba su d'ebi 'ya'yansu sun kai su garuruwansu na asali ba. Wasu dai sun yi 'ko'kari sun shaidawa 'ya'yan nasu sunayen garuruwansu - da yawa ba su samu damar yin hakan ba saboda wasu dalilai da Allah kad'ai Ya sani. Don haka, Jasawa na zamani da yawa wad'anda sune alumma a mataki na uku ko na hud'u, ba su san garuruwan da iyayensu suka samo asali ba.

Bugu da 'kari, kasancewar al'ummar Hausawa Musulmi ne ya sa duk inda mutum ya je ya zauna yana d'aukar wannan wuri tamkar garinsu. A wurin su 'kasa ta Allah ce mai fad'i, duk inda mutum ya samu kanshi sai kawai ya du'kufa bautar Allah da hidimar kyautatawa bayin Allah.

Wad'annan mutane da suka zo, ko aka d'ebo su aka kawo su, su ne suka sadaukar da rayuwar su da duk abin da suka mallaka don gina wannan wuri da ake kira Jos. Kai hatta d'an ci-ranin da ba ya yin wata biyar a garin ya na bayar da gudummawa gagaruma wajen ciyar da wannan gari gaba ta fuskar tattalin arzi'ki.

Monday, March 19, 2007

Wa'ko'kin Goethe a Hausa: Yadda Hausa ke 'kara buwaya


Daga Muhammad K. Muhammad


Johann Wolfgang von Goethe wani bawan Allah ne da ya yi rayuwa a 'kasar Jamus a 'karni na 18 zuwa na 19 (1749-1832) miladiyya. Saboda shaharar Goethe a fagen adabi, a iya kamanta shi da Shakespeare na 'kasar Ingila. Ko da yake Goethe ya shahara sosai a fannin rubutattun wa'ko'ki, shi fasihi ne a 'bangarorin rayuwa daban-daban.



Baya ga wa’ko’ki, Goethe ya yi fice a rubutun wasan kwaikwayo, da ‘kagaggen labari. Sannan kuma ya yi suna matu’ka a harkar binciken kimiyya, musamman nazarin tsirrai, wanda ya shiga yi sakamakon sha’awar da lura da halittu ya saka masa. Sannan kuma Goethe ya la’kanci harsunan Faransanci, Ingilishi, Italiyanci, Latin, Girkanci, da Ibraniyanci (Hebrew). Burinsa a rayuwa shi ne, ya kasance abin misali ga sauran jama’a a kan dukkan al’amuran rayuwa.
Masana sun bayyana cewa yadda Goethe ya fad’ad’a ayyukansa ya sanya ya samu abin cewa a kan dukkan ra’ayoyi ko mahanga daban-daban na zamaninsa, sannan kuma ya taryi abin da zai zo a zamanin da muke ciki a yau. Wad’annan masana sukan bayar da misali da wani littafin ‘kagaggen labari da ya rubuta a 1829 mai suna Wilhelm Meisters Wanderjahre, oder Die Entsagenden (Yawon Duniyar Wilhelm Meisters ko Ma’kamarsa), inda yayi magana a kan ci gaban masana’antu da kuma ‘kwarewa ta musamman a wani ‘bangare.
Tasirinsa a kan harkar adabi a ‘kasar Jamus da sauran ‘kasashe masu amfani da harshen Jamusanci ba ya misaltuwa, kuma har gobe ruwa na maganin daud’a, ma’ana har gobe tasirinsa a kan adabin Jamusanci bai gushe ba. Shi ya sa ma aka sanya wa babbar cibiyar al’adu ta ‘kasar Jamus suna Cibiyar Goethe (Goethe Institut).
Goethe ya fi shahara a duniyar adabi da littafin da ya rubuta na wasan kwaikwayo cikin wa’ke mai suna Faust. Faust labarin wani mutum ne masanin kimiyya da sihiri, wanda ya rayu a ‘karni na 16, wanda kuma Goethe ya ala’kanta shi da gwagwarmayar rayuwa ta d’an-Adam, da al’umma, da kuma siyasa. An buga wani ‘bangare na wannan labari a shekarar 1790, kashi na d’aya na littafin kuma an buga shi a 1808, kashi na biyu kuma bayan rasuwar Goethe a 1832.
A cikin shahararrun wa’ko’kin da Goethe ya rubuta, akwai kundin wa’ko’kinsa (wato diwani) wanda ake kira West-östlicher Divan (Diwanin Gabas da Yamma). A cikin wannan littafin wa’ko’ki, Goethe ya bayyana irin tasirin da mawa’kin nan na ‘kasar Farisa (Iran) mai suna Muhammad Shamsuddin Hafiz ya yi a kansa. Babu shakka baituka da dama a cikin wannan littafi sun yi kama da wasu a cikin Diwan na Hafiz. Hasali ma a bangon wannan littafin na Goethe, a ‘bangaren dama, an rubuta sunan littafin da Jamusanci, yayin da a ‘bangaren hagu kuma aka rubuta fassararsa da Larabci, ko da ya ke fassarar ba ta bayar da ma’anar Jamusancin sosai da sosai ba.
Ga wanda ya rubuta wannan fassara (Diwanin Gabas na Marubucin Yamma) littafin na Gabashin Duniya ne yayin da marubucinsa kuma d’an Yammacin Duniya ne. A zahiri kuma ga wasu daga cikin manazarta, haka al’amarin yake don kuwa Goethe ya yi amfani ne da salo irin na Hafiz, da tunani irin nasa. Daga cikin babi-babi na wannan littafin har akwai wanda Goethe ya sanyawa suna Buch Hafiz (wato Babin Hafiz) inda ya ke cewa: “Kai nake kwaikwayo matu’ka/Ni ma da an kai min baiwa/Da sanin littattafai tsarkaka”.
West-östlicher Divan ya ‘kunshi fiye da wa’ko’ki 200 wad’anda aka karkasa su zuwa babi 12. Ko wanne daga cikin babin kuma an ba shi suna biyu, d’aya na Jamusanci, d’aya na Farisanci. Misali, babin farko a West-östlicher Divan, sunansa Buch des Sängers (Littafin Mawa’ka) a Jamusanci da kuma Moganni Nameh a Farisanci. Haka nan kuma akwai Buch der Betrachtungen/Tefkir Nameh, Buch der Sprüche/Hikmet Nameh, da sauransu.
Wasu masana sun bayyana cewa Goethe ya rubuta West-östlicher Divan ne saboda wata matsananciyar soyayya da ya afka. Goethe ya yi soyayya da mata da d’an dama wad’anda suka had’a da Charlotte von Stein, wadda ta grime shi da shekara bakwai, Christiane Vulpius (wadda ta haifa masa d’a mai suna August), Minna Herzlieb, da kuma Marianne von Willemer, budurwar da ya rubuta West-östlicher Divan saboda ita, ita ce kuma ta fito a littafin da sunan Suleika, kamar yadda Charlotte von Stein ta fito a Faust.
A d’angon ‘karshe na d’aya daga cikin wa’ko’kinsa, Goethe yana cewa: “Rad’ad’in ‘kauna ya nemi wuri/Inda zai ke’be don samun kad’aici/Nan ya bid’o zuciya ta kango/Sai ya shige a ciki ya la’bo.” Haka nan littafin ya yi magana a kan al’amuran addini, inda ya ‘kunshi kalamai da ‘kissoshi daga Baibul da Al’kur’ani. Daga cikin sunayen da Goethe ya ambata akwai Annabi Adamu, Annabi Ibrahim, Annabi Isa (AS) da Annabi Muhammadu (SAW). Wasu manazarta na ganin cewa abin da ya had’a Goethe da Hafiz shi ne irin tunanin bijire wa tsarin da al’ummar Turai ta ke kai a wancan zamanin da Goethe ya rayu, kamar yadda Hafiz ma ya bijire wa tsarin da shi ma ya gada.
Amma idan aka je aka zo, ana kallon wannan kundi na Goethe a matsayin wani mataki na had’a kan gabashi da yammacin duniya duk da irin bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Wannan ne ma ya sa ‘kungiyar UNESCO ta gina wasu kujeru masu fuskantar juna a garin Weimar da ke ‘kasar Jamus, a bayan gidan Goethe don tunawa da wad’annan marubuta guda biyu.
Saboda muhimmancin harshen Hausa, ba kawai ga ‘kasar Jamus ba, har ma da matsayin harshen a wannan mu’kabala ta gabas da yamma, yanzu wasu manazarta sun fassara West-östlicher Divan zuwa harshen Hausa. Wannan littafi mai suna Waqoqin Goethe, wani tsohon Farfesa a Sashen Nazarin Harsunan Afirka a Jami’ar Goethe da ke Frankfurt, Herrmann Jungraithmayr, shi ne ya fassara shi tare da had’in gwiwar wani abokin aikinsa, Yahaya Ahmed. A mu’kaddimar littafin, marubutan sun kawo tarihin wa’ko’kin, muhimmancin harshen Hausa ga adabi, da kuma matakan da suka bi wajen yin fassarar.
A 'karshen littafin kuma, mai ‘kunshe da wa’ko’ki 20 daga Divan na Goethe, manazartan sun kattaba wata wa’kar, tasu.




Wannan nazari ya fara fitowa ne a jaridar Aminiya ta 16 ga Maris, 2007.