Monday, February 04, 2008

Albasa (Ba) Ta Yi Halin Ruwa (Ba)


Masu iya magana ne ke cewa “Albasa ba ta yi halin ruwa ba” idan aka samu wani mutum ya sa'ba d'abi’ar da ake zaton gani a wurinsa ko wurinta (wanda ya kamata a ce ta/ya gada). Idan kuwa albasar ta yi halin ruwa, sai ka ji sun ce “Barewa ba ta gudu d'anta ya yi rarrafe”.
Wata'kila idan mutum ya dubi hoton da ke saman wannan ma'kala (idan shugaban 'kasa Malam Umaru 'Yar'aduwa ke gabatar da 'yarsa ta cikinsa [ta gefen hagu] ga Sakatariyar Harkokin Waje ta Amurka, Condoleezza Rice) ya yi tambaya: “Shin albasa ta yi halin ruwa, ko ba ta yi ba?” Ha'ki'ka na ga wani marubutci ya yi 'ko'karin yin wannan tambaya ko da ya ke bai bayar da amsa ba.
Lokacin da uwar gidan Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Zainab Shekarau, ta kai ziyara Katsina don taya iyalan Malam Umaru Musa 'Yar’aduwa murnar cin za'ben shugaban 'kasa da ya yi, ta bayyana cewa ala'kar su da nata iyalin ba a fagen siyasa ta samo asali ba. A cewar ta sun sha had'uwa da uwar gidan Malam Umaru a wuraren da'awa. Ma’ana su kan had'u a wuraren da a kan yi kira don shiryar da jama’a zuwa ga karantarwa irin ta addinin Musulunci!
A nan idan muka kwatanta irin shigar da mukan ga Hajiya Turai ta yi a hotunan jaridu da talabijin da irin suturar da Musulunci ya karantar da mata su sanya, ma iya cewa uwar gidan Shugaban 'Kasar ba ta aiki da abin da ta ke fadi? Wata'kila ma iya cewa ai uwar gidan Shugaban na suturta jikinta, illa wani 'bangare na wuyanta da ya kan fito jifa-jifa (wata'kila don a ga irin gwal d'in da ta sanya mai tsada), don haka tana aikata abin da ta ke fad'i.
Idan haka ne, ya zamu yi da maganar da a kan ce wai “sai gida ya 'koshi a kan bai wa waje”, ko kuma “tarbiyya daga gida ake faro ta”? Ya aka yi Hajiya Turai ta yi ta yawon da’awa don shiryar da wad'ansu amma ta kasa shiryar da 'ya'yanta? Don kuwa ba yarinyar da muke gani a wannan hoto na sama ce kad'ai ta ta'ba shiga mai ayar tambaya ba. Kwanan baya mutane da yawa sun yi ta surutu a kan irin tufafin da d'aya 'yar tata wadda ta auri wani gwamna ta sanya lokacin auren nata.
Amma fa kar mu manta cewa uba shi ake tsammani zai yi tsayin daka don tarbiyyantar da 'ya'yansa. To mai ya hana Malam Umaru yi wa 'ya'yansa tarbiyya musamman ta 'bangaren irin tufafin da ya dace su sanya?
A nan yana da kyau mu tuna cewa idan ana ambatar labarin rayuwar Malam Umaru a kance lokacin yana ala’kanta kansa da 'bangarancin siyasa da a turance ake kira left (wato hagu). Sannan kuma ana nuna cewa Marigayi Dokta Bala Usman (lokacin yana tashen ra’ayi irin na gurguzu) ya yi tasiri matu'ka a kan Malam Umaru. A sanin kowa ne kuma cewa zai yi wuya ka samu mai ra’ayin gurguzu da ba ya ra’ayin Makisanci (Marxism).
To ko dai da shi bai d'au wannan ra’ayi na Makisanci ba, uban da zai 'kyale 'yar sa tana irin wannan shiga to wata'kila irin mutanen nan ne da Mallam Muhammad Bin Usman ya kira 'yan boko a'kida*. Ke nan an d'auki boko da muhimmancin da ya sa ake ganin cewa wayewa ta 'kunshi d'abi’u irin na Yahudu ko da kuwa sun sa'ba da al’adun gado.
Amma fa kar mu manta da maganar da Hausawa kan yi: “Ka haifi yaro ba ka haifi halinsa ba”. Ko wannan na iya zama dalili da za mu iya cewa iyaye su na da uzuri idan 'ya'yansu suka fara yin shigar da ba ta dace ba? Hasali ma a iya bayar da misali (musamman ta 'bangaren Hajiya Turai) da Annabi Nuhu da d'ansa.
Ni a gani na wannan ba uzuri ba ne. Don kuwa in har mutum ya tsaya tsayin daka wajen tarbiyyar 'ya'yansa, da addu'ar Allah Ya shirya su, to zai yi wuya a ce dukkansu sun fand'are. Kar mu manta - kamar yadda muka fad'a a baya - wannan yarinya ba ita kad'ai ce kafofin yad'a labarai suka haska mana hotonta da shigar da ba ta dace da mu ba. Ke nan ko dai albasa ta yi halin ruwa (ma’ana barewa ba ta yi gudu d'anta ya yi rarrafe ba) ko kuma mai dokar barci ya 'bige da gyangyad'i.
Abin nufi shine Hajiya Turai ta kasa shiryar da iyalinta (alhali ko Manzon Allah [SAW] kafin a ba shi umarnin kiran kowa da kowa sai da aka fara umartar sa ya kira danginsa na kusa) ta fita shiryar da na waje. Abin tambaya a nan shi ne: “Ta yaya wanda ya kasa jagorancin gidansa zai jagoranci 'kasa irin Nijeriya?
______________________________________
* Mallam Muhammad Bin Usman ya yi bayanin cewa 'yan boko sun kasu uku: (1) 'Yan boko a'kida/addini, (2) 'Yan boko sana'a, da kuma (3)'Yan boko manufa.