Wednesday, April 23, 2008

Birnin K’udus: Mallakin Yahudawa ko Musulmi?

Sunan Littafi: 'Kudus Birni Ne Na Musulunci
Marubuci: Nuruddeen Ibrahim Kano da Ustaz Abu Hanifa Jibreel Assalafi.
Mai Sharhi: Bashir Yahuza Malumfashi.
Kamfanin Wallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano.
Shekarar Wallafa: 2008.
Yawan Shafuka: 90.
Farashi: Ba a fad'a ba.
Kowace a'kida kake bi, kowane addini kake bi, idan dai saukakku ne daga Allah a tarihance, to birnin 'Kudus abin ala'kantawarka ne. Wannan kuwa haka yake a tarihance, domin kuwa muhimman, bun'kasassun, ingantattun addinan nan uku da suka shahara kuma suka bun'kasa a duniya, suna da muhimmin tasiri da tarihi da ala'ka da birnin 'Kudus. Wad'annan addinai kuwa kamar yadda muka sani, su ne Yahudanci, Kiristanci da kuma Musulunci. Dalili ke nan wad'annan mawallafa suka gudanar da ingantaccen bincike, suka rubuta wannan littafi da muke sharhi a yau. Kuma babu shakka ba su yi 'kasa a gwiwa ba, domin kuwa sun tabbatar kuma sun gabatar da gamsassun hujjoji da bayani da suka nuna cewa, lallai 'Kudus birni ne na Musulunci.
Hujja kyakkyawa kuma mai gamsarwa da za ta 'kara tabbatar da jigo da i'kirarin wannan littafi ita ce, dukkan Annabawan da Allah (SWT) Ya aiko a bayan 'kasa Musulmai ne, balle kuma Manzannin da suka zo da muhimman littattafan Attaura (Musa, Alaihis Salam), Injila (Isa, Ruhullah) da Al'kur’ani (Muhammadu, Sallallahu Alaihi Wasallam), dukkansu suna da ala'ka da wannan muhimmin birni na 'Kudus.
Idan muka yi nin'kaya cikin littafin nan, da farko dai za mu iya cewa an yi masa aikin wallafa mai inganci, musamman ta fuskar d'ab’insa, wanda aka yi da haruffa masu girma, ta yadda kowa zai iya karanta shi cikin sau'ki. Na biyu, an yi amfani da takarda mai inganci, wadda ta sha bamban da wadda wasu mawallafa ke amfani da ita mai araha, wacce ba ta dace da buga littafi mai muhimmanci ba. Na uku kuma, an yi aiki mai yawa, ta yadda aka tsarkake littafin daga manyan kura-kuran d'ab’i da suka zama ruwan dare a mayawaitan littattafan Hausa. Na hud'u, an yi amfani da salo da sigar wallafa ta zamani, ta yadda aka bi 'ka’idojin wallafa kamar yadda ake bu'kata; wannan kuwa ya had'a da samar wa littafin Lambar Littafi Ta Duniya. Yin haka ma ya 'kara bambanta littafin daga mafi yawan kwashi-kwaraf d'in littattafan da wasu marubuta ke wallafawa ta hanyar yin wallafar tuwona-maina, ko kuma mu ce dakan-d'aka-shi'kar-d'aka-tankad'en-bakin-gado.
Littafin dai yana 'kunshe da gabatarwa har kala uku daga shafi na biyar zuwa na goma. Wannan kuwa sun had'a da gabatarwar kamfanin wallafa da gabatarwar marubuci na farko da kuma gabatarwar marubuci na biyu, wanda ya kasance mai fassara.
Daga shafi na goma sha d'aya zuwa na sha hud'u kuwa, an yi bayani ne game da abin da marubutan suka kira, Mashigar Maudu’i, inda nan suka yi ta'kaitaccen bayani game da ita kanta daular Falasd'inu, inda nan birnin 'Kudus yake da kuma sauran muhimman garuruwan da ke cikin yankin. Bayanin kuma ya had'a har da kawo taswirar 'kasar Falasd'inu, wadda ke d'auke da sunayen garuruwan 'kasar gaba d'aya.
Daga shafi na goma sha biyar zuwa na ashirin da d'aya kuwa, ya kasance Fasali Na Farko, inda aka yi bayani game da tarihin kafuwar birnin 'Kudus. Haka kuma an yi dogon bayani game da fad'in birnin da yanayinsa; inda a ciki aka zayyana cewa birnin na d'auke ne da 'kofofi har guda bakwai, wad'anda suka had'a da 'kofar Amuud, 'kofar Saahirah, 'kofar Magaaribah, 'kofar Annabi Dawud, 'kofar Khalil da kuma Sabuwar 'Kofa. Haka kuma, an kawo tarihin tsofaffin mazauna birnin na 'Kudus, inda aka tabbatar da cewa al’ummomi biyu ne asalin mazauna birnin, wad'anda suka kasance al’ummar Kan’ana da ke zaune a tsakiyar Falasd'inu da kuma Falasd'inawa da ke zaune a gefen ruwa daga shiyyar kudu.
Daga shafi na ashirin da biyu zuwa na arba’in da biyu na littafin kuwa, nan mai karatu zai tsinkayi Fasali Na Biyu, inda aka yi bayani dalla-dalla game da matsayin birnin 'Kudus a addinance. An fayyace falalar 'Kudus, kamar yadda Al'kur’ani ya bayyana a cikin wasu ayyanannun ayoyi. Haka kuma, an kawo falalar birnin 'Kudus a cikin Sunnah tsarkakakkiya, inda kuma marubutan suka kawo wasu ingantattun Hadisan Manzon Allah (SAW), inda ya yi magana game da falalar birnin ga Musulmai da Musulunci. Sun kawo tarihin yadda aka yi har Annabi Ibrahim (AS) ya yi hijira zuwa birnin na 'Kudus, inda tarihin ya nuna cewa ya yi wannan hijira ne da shekaru dubu biyu kafin haihuwar Annabi Isa (AS). A nan ne kuma marubutan suka kawo hujjar da ta tabbatar da cewa lallai Annabi Ibrahim (AS) ba Bayahude ba ne kamar yadda Allah (SWT) Ya tabbatar a cikin Al'kur’ani mai girma (Al-Imran, 67-68).
Duk dai a cikin wannan fasali na biyu na littafin, an kawo bayanin wasu wurare masu tsarki na Musulunci a birnin 'Kudus. Wad'annan kuwa sun kasance Masallacin 'Kudus, Hubbaren Sakhara da kuma Masallacin Sayyidina Umar (RA). Marubutan sun yi 'ko'karin buga hotunan Masallacin na 'Kudus da kuma Hubbaren Sakhara a shafi na talatin da biyar na littafin, kuma hotunan duk suna cikin kala.
Wannan fasali na biyu bai kammala ba sai da marubutan suka kawo tarihi game da ’ya’yan Isra’ila, wato Annabi Ya'kuba (AS) ke nan. Sun kuwa kawo gamsassun bayanai tare da ayoyin Al'kur’ani da suka kafa hujja da su. Babu shakka, hakan da suka yi ya 'kara wa tarihin inganci, wanda zai gamsar da masu bincike; wanda haka kuma zai kauce wa shakku.
Abu ne sananne cewa, babu yankin da ya sha gwagwamayar ya'ki da tashin hankali, kuma yake cikin kan ganin ya'ke-ya'ke har yau d'in nan, kamar yankin 'Kudus, wanda haka ya sanya babu yadda za a yi tarihin yankin ya kammala ba tare da kawo bayanan ya'ko'kin da suka faru a yankin ba. Babu mamaki da marubutan littafin suka ware Fasali Na Uku na littafin, wanda ya faro tun daga shafi na arba’in da uku har zuwa shafi na saba’in da d'aya, inda nan ne aka ba da tarihin yadda aka ci garin 'Kudus da ya'ki, sannan kuma aka bayyana dukkan ya'ko'kin da aka gwabza a cikinsa.
An yi bayani game da yadda aka bud'e birnin 'Kudus ta hannun Umar 'Dan Khad'd'ab (RA), wanda shi ne ya zama Khalifa bayan rasuwar Khalifa Abubakar (RA). Daga nan kuma sai bayanin Ya'kin Kuros, wanda Turawa suka assasa wa 'Kudus. Nan ma an yi bayani dalla-dalla, aka bayyana duk yadda ta kwaranye. Daga nan kuma sai suka kawo tarihin yadda aka bud'e 'Kudus ta hannun bawan Allah, Salahuddin Ayyubi.
Daga shafi na saba’in da biyu zuwa shafi na tamanin da takwas kuwa, nan aka kawo Fasali Na Hud'u kuma na 'karshe a littafin. Nan ne kuma aka kawo halin da birnin 'Kudus yake ciki a yau. A ciki ne aka yi bayanin yadda aka yahudantar da birnin na 'Kudus, wanda haka ya faru bisa makircin da Yahudawan duniya na zamani suka yi had'in baki, suka mallake yankin a yau. Haka kuma, an kawo bayani da tarihin yadda aka Kiristantar da birnin na 'Kudus. Sannan kuma daga 'karshe aka kawo tarihin dalili da kuma abin da ya sanya Musulmi suka 'kaurace wa birnin 'Kudus, duk kuwa da cewa su ne suka fi cancanta da mallakarsa.
Daga shafi na tamanin da bakwai kuwa zuwa na casa’in, an kawo marufin da ya rufe littafin, inda kuma aka kawo jerin gwanon sunayen littattafan da marubutan suka gudanar da bincike da nazarinsu don rubuta wannan littafi.
Kamar yadda muka gabatar a baya, babu shakka samar da wannan mashahurin littafin a yau, zai tada tsimin Musulmi domin su gane muhimmancin birnin 'Kudus a gare su, sannan su yi ho'b'basan kawo d'auki na yadda za su sake mallakar abinsu, wanda magabatan 'kwarai sun dad'e da yin kira ga haka. Haka kuma littafin ya yi 'ko'karin daidaita tarihi na gaskiya, inda suka wanke kuma suka wancakalar gur'bataccen tarihin da Yahudawa da ’yan kanzaginsu suka bayyana game da yankin.
Babu shakka, masana sun sha nanata cewa, hannun marubuci makaho ne, kamar kuma yadda suka tabbatar da cewa littafi d'aya ne a duk duniya da babu kure a cikinsa, wanda ya kasance Al'kur’ani mai girma. Don haka, bayan na kammala karanta littafin nan, duk da cewa an yi 'ko'kari sosai wajen kauce wa bayyanar kura-kurai, to amma da 'kyar da ji'bin goshi idanuwana suka kallo wasu daga abin da nake ganin cikashi ne ga littafin, duk da cewa ba su taka kara sun karya ba.
Abu na farko shi ne, hoton bangon littafin. A gani na, maimakon hoton Hubbaren Sakhara da aka sanya a bangon littafin, ya kamata a ce hoton Masallacin 'Kudus aka sanya. Domin kuwa, a can baya, an samu Yahudawa suna yad'a hoton hubbaren a matsayin Masallacin 'Kudus, wanda haka ya sanya wasu Musulmin suka d'auka kamar hubbaren ne ma masallacin. Da an yi amfani da hoton Masallacin, da ya fi tasiri wajen daidaita tunanin wasu da suka zaci hubbaren ne masallacin.
Kuskure na biyu da na ci karo da shi a littafin shi ne, yadda aka yi ta amfani da 'kananan ba'ka'ke wajen rubuta kalmomin musulmi da musulunci a dukkan shafukan littafin. Ya dace a ce an yi amfani da manyan ba'ka'ke kamar haka: Musulmi, Musulunci, domin kaurara muhimmancin sunayen.
Haka kuma, a shafi na 35, an samu kuskuren rubuta sunan Masallacin 'Kudus, inda harafin ('K) ya kasance ba a canza shi zuwa harafin Dokta Abdallah ba.
A shafi na 89 zuwa na 90 kuwa, inda aka kawo sunayen littattafan da aka duba, an kawo su ne da haruffan Larabci, maimakon a kawo su da haruffan Hausa, tunda da harshen Hausa ne aka fassara littafin.
Duk da wad'annan ’yan kura-kurai da suka bayyana a littafin, babu shakka dole a jinjina wa 'ko'karin marubutan nan, domin kuwa sun jaddada kuma sun tsarkake tarihi, wanda ba 'karamin makami ba ne na farfaganda da Yahudawa suka dad'e suna amfani da shi wajen cutar da Musulunci da Musulmi.

Wassalam.
Bashir Yahuza Malumfashi
Aminiya, Abuja.