Monday, June 16, 2008

Ingiza Mai Kantu Ruwa

Kwanan baya na hau bas zan tafi ofis. Da yake a wurin tsayawar ‘yan bas d'in na hau, sai da motar ta cika sannan muka tashi. Cikar kuma har ta batse, domin kuwa yaron mota a kan inji (maneji) ya ke.
A bisa al’ada, ‘yan bas sukan d'ebi mutane su ma'kare bas d'in: na ma ta'ba jin wani kwandasta (conductor) yana cewa ‘mota roba ce, ba ta cika’. Amma a Abuja yin hakan had'ari ne domin idan jami’an duba lafiyar motoci (VIO) su ka yi ido hud'u da direban da ya cika mota ya d'ora kwandasta a kan injin to sai ya yi ta wasu kud'ad'e masu d'an kauri—sai ya yi asara na ke nufi. Ga VIO kuma ba kamar ‘yan sanda ba; ba sa kar'bar na goro su 'kyale mutum.
Muna cikin tafiya sai ga motar VIO kamar daga sama! Muna isowa jankshan aka yi rashin sa’a jami’i mai bayar da hannu ya tsayar da motoci kuma babu yadda za a yi direban bas d'in nan ya juya ko ya canja hanya don ya tsere. Jami’an VIO suka yi masa nuni ya tsaya, amma wasu fasinjoji da ke motar, musamman wasu ‘yan mata su biyu, su ka ba shi shawarar kar ya tsaya. Lokacin da aka saki hanya, direban VIO ya nunawa direban bas ya fi shi iya mota don kuwa ya sha kansa ya hana shi guduwa.
Da direban bas ya ga ba sarki sai Allah, sai ya tsaya. 'Daya daga cikin jami’an VIO ya fito, sai muka ga dattijo ne; ga alama ya haura shekara sittin. Nan fa ‘yan matan nan da suka zuga direban bas suka yiwa wannan dattijo ca, suna cewa “Tsoho da kai ka zo kana neman cin-hanci. Me zai hana ka yi ritaya ka koma 'kauyen ku ka yi noma? Ire-irenka, tsoffin da suka 'ki yin ritaya, ku ne ku ka hana mu samun aiki”. 'Daya daga cikin ‘yan matan ta d'aga wani 'katon ambulan da ke hannunta ta 'kara da cewa, “Dubi takarduna, na gaji da yawon neman aiki ban samu ba saboda tsoho da kai ka 'ki ka yi ritaya a samu gurbin da za a d'auke ni”.
Alamu kuma sun nuna cewa d'aya jami’in ya fi wannan dattijon a mu'kami duk da shi matashi ne. Kuma ga alama ya yi tunanin tausayawa direban ya 'kyale shi, amma sai dattijon ya shaida masa abin da ‘yan matan suke fad'a; don haka jami’in ya canja shawara.
Daga 'karshe dai, ba girma ba arzi'ki, jami’an VIO su ka tilasta fasinjoji sauka daga mota domin a cewarsu za su tafi da direban nan ofishinsu ya je ya yi bayani. Shi kuwa kwandasta, tilas ya zaro kud'aden jama’a ya dan'kawa kowa abin da zai 'karasa da shi inda ya yi niyyar zuwa.
Had'ama ta sa direban bas ya yi asara goma da goma: zai yi asarar kud'ad'en da ya tara a wannan yini, ga shi kuma kud'in da ya kar'ba a hannun fasinjojin da su ka zuga shi ya 'ki tsawa dole ya mayar masu da abinsu; bugu da 'kari, fatan samun wasu kud'ad'en a wannan yinin yana dab da yankewa a zuciyarsa kwata-kwata, domin idan jami'an nan suka tafi da shi to sai abin da hali ya yi, ma'ana sai sanda aka ganshi. Mu ma ko ba komai an 'bata mana lokaci, sannan an sanya mu dole mu hau wata motar wadda da 'kyar mu ka samu.
Babu shakka masu cewa “A bi doka a zauna lafiya” sun yi gaskiya. Sannan kuma duk wanda ya biyewa mata, idan bai yi a hankali ba, to sai ya yi da-na-sani (ba ina nufin duk mata haka su ke ba; sai dai yana da kyau a ri'ka sara ana duban bakin gatari).
Ita kuma hukuma, wajibi ne ta tashi tsaye don gyaran tattalin arzi'kin 'kasa, domin talauci na d'aya daga cikin dalilan da suka sa mutane ke karya doka a 'ko'karin neman kud'i ta ko wacce irin hanya. Bugu da 'kari, hakan zai sa aikin yi ya samu, a rage yawan matasa masu zaman banza, da wad'anda suka galabaita wajen neman aiki har suka fara shiga wani hali da suka fara daina ganin kowa da gashi. Idan ba a yi hankali ba ma, daga nan sai su fara kai duka, ko ma abin da fi haka. Allah Ya sawwa'ke.