Saturday, November 15, 2008

Bafulatanin Yola Ya Doke Hausawa a Gasar Adabin Hausa


Wani Bafillace daga Yola ta Jihar Adamawa ya doke Hausawa a gasar Adabin Hausa inda ya lashe kyautar lnjniya Muhammad Bashir 'Karaye kan Adabin Hausa ta bana (2008).
Littattafai 15 ne suka shiga wannan gasa, wad'anda shida daga cikinsu suka tsallake sirad'i na farko.
Wad'annan litlattafai shida su ne: Halin Rayuwa na Aliyu Z. Mainasara, da Kowa Ya Bi na Abdurrashid Sani Isa Nijeriya, da kuma Baki Abin Magana na Dala'ilu Bobboji. Sauran su ne littafin Ibrahim Birniwa mai suna Garinmu Da Nisa, da na Muhammad Lawal Barista, Ba'kin Kishi, da kuma na Nazir Adam mai suna Murmushin Alkawali.
Zakarun gasar su ne Dala'ilu Bobboji, mai littafin Baki Abin Magana, wanda ya yi na d'aya; da Ibrahim Birniwa, mai Garinmu Da Nisa, wanda ya yi na biyu; sai kuma Muhammad Lawal Barista, marubucin Ba'kin Kishi.
Zakaran gasar ta bana, Dala'ilu Bobboji, ya bayyana cewa ya rubuta Baki Abin Magana ne saboda takaicin da ya jima yana yi, ganin yadda littattafan Hausa suka zamo tamkar jarida.
"In ka d'auki littafi—abin mamaki—kana karanta shi kamar kana karanta jarida. Sai ka rasa inda aka faro labarin, ka rasa inda aka nufa, ka rasa kuma 'karshensa. Labarin ne za ka karanta ba ma'ana: daga soyayya sai soyayya; babu wani abin da zai burge ka sai soyayya kawai. Ni ma littafina akwai soyayya, amma na tsara shi ne da tsari, kuma yadda al'adar Bahaushe take", inji Malam Dala'ilu.
Marubucin ya kuma 'kara da cewa yadda ake d'aukar al'adun waje ana 'ko'karin 'ka'kaba su a cikin na Hausa da 'karfi da yaji abin takaici ne. “Shi ya sa na ce me zai hana na zauna na rubuta littafi irin na wad'anda suka yi na baya, domin da ka dauki littafi irin nasu kana karantawa, in dai kai makarancin Hausa ne, to za ka san ba ka 'ketare iyakar al'adarmu kamar yadda na zamani suke yi ba", inji Malam Dala'ilu.
Shi dai littafin Baki Abin Magana, an rubuta shi ne a bisa irin salon littafin Abubakar Imam, Magana Jari Ce, wanda d'aya ne daga cikin littattafan adabin Hausa mafi shahara, kuma d'aya ne daga cikin littafai uku da malamin ya rubuta a shekarar 1986 don shiga wata gasar rubutun adabi. Ya kuma rubuta wad'annan littattafai ne cikin wata bakwai.
An haifi Dala'ilu Bobboji a garin Song na Jihar Adamawa a shekarar 1966. Ya halarci Kwalejin Je-ka-ka-dawo ta Gwamnati da ke Yola (Yola Government Day College) da kuma Kwalejin Nazarin Shari'a ta Yola (Collegc of Legal Studies, Yola), inda ya fita da difloma kan Shari'a da Dokokin Zamani (Shari'ah and Civil Law).
Bayan kammala karantunsa, Malam Dala'ilu ya yi aiki a Kotun Daukaka Kara ta Shari'ar Musulunci da ke Yola, kafin ya koma Kwalejin Nazarin Shari'a, inda ya yi aikin karantarwa.
Ita dai wannan kyauta ta Adabin Hausa ta 'Karaye, matar marigayi Injiniya Muhammad Bashir 'Karaye, Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, ce ta assasa ta bara don 'kara 'kwarin gwiwa ga marubuta wajen rubutu a cikin harsunanmu na gida. Wanda ya zo na d'aya a gasar ya samu tsabar kud'i Naira dubu 150; wad'anda suka zo na biyu da na uku kuma sun samu Naira dubu 100 da Naira dubu 50.
'Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) da had'in gwiwar Gidauniyar Injiniya Muhammad Bashir 'Karaye suka d'auki nauyin shiryawa, tantancewa, da kuma bayar da wannan kyauta.
Daga cikin manyan ba'kin da suka halarci wajen bayar da kyaututtukan a Abuja har da tsohon ministan ma'adanai, Alhaji Bashir 'Dalhatu, da tsohon Babban Mai Shari'a na Nijeriya, Mai Shari'a Muhammad Lawal Uwais, da shugaban 'Kungiyar Marubuta ta 'Kasa kuma tsohon d'an Majalisar Wakilai, Dakta Wale Okediran da kuma wani malami a sashen Nazarin Harshen Ingilishi a Jami'ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Dakta E.E. Sule.
Wad'anda suka yi al'kalanci da tantance littattafan da suka cancanci yabo su ne Babban Daraktan Hukumar Talabijin ta Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Dachia da kuma Malam Kabir 'Dan'asabe, malami a Sashen Nazarin Harshen Hausa a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Zuba, Abuja.

Daga jaridar Aminiya, 3-9/11/1429 (31/10-6/11/2008)