Tuesday, April 21, 2009

Kowa Ya Yi Da Kyau

Tsintacciyar Mage Ba Ta Mage


Sarautar da babu al'kali, ba yari babu maji-dad'i ba makama;
Na ji mutane suna ta cewa
Wagga sarauta wacce iri ce?


...

Kowa zai yi kira nai
Yayyi kira nai da inkiya tai
In ko ba ku kira nai da inkiya tai
Ga wani suna za ni rad'a mai:
Ya zama sarki na tashi-bi-su
” —Musa 'Dan 'Kwairo


Duk inda aka samu halittu masu halayya ko kamanni iri d'aya, to za a same su da wasu d'abi’u wad'anda suke bambanta su da sauran halittu. Wad'annan d'abi'u su ne fid'irar da Allah Ya halicce su a kanta, wadda suke gudanar da rayuwarsu ta hanyarta. Haka nan kuma bisa ga wannan fid'ira, wad'annan halittu kan samar wa kansu wani tsari na tafiyar da al’amuransu yadda babu wani 'bangare nasu da zai yi bore, ko ya koka cewa an yi abin da bai dace ba. Wannan ya sa duk sanda wani ba'kon al’amari ya shigo, sai ka ga hankali ya tashi; tamkar sartse ne, inda wani abu da ba 'bangare ba ne na wani jiki ya kan shiga jikin, sai ka ga har zazza'bi ya kan sanya masa.

Wannan shi ne abin da ya 'kara fitowa fili lokacin da aka zo nad'a sabon Gbong Gwom—wato Sarkin Birom a Jihar Filato—bayan mutuwar tsohon. Kasancewar wannan sarauta ba ta da asali balle tushe, mutanen da suka 'ka'kabawa kansu ita ba su da wani tsari na gado wanda zai zama manuni dangane da yadda za a maye gurbin sarakin da aka rasa. Wannan babban gi'bi ya sanya duk sanda aka zo nad'a sabon Gbong Gwom sai ka ji ana 'korafi; wasu na cewa gadon kujerar ya kamata a yi, wasu na cewa a’a kamata yayi ta ri'ka zagawa a tsakanin dagatai ko masu unguwannin 'kauyukan da 'yan 'kabilar Birom d'in suka samo asali, wasu ma cewa suke a’a kamata ya yi a ce sarautar tana kewayawa tsakanin 'kabilun da ke 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa, don kuwa an ce Gbong Gwom Jos—ke nan idan dai sarautar ta Jos ce, to wajibi ne duk 'kabilun Jos su zamo suna da gado a cikinta.

To amma kasancewar sarautar ba ta da tushe, ba ta da asali, hasali ma da mugunyar manufa aka 'kir'kire ta, dole ne a ri'ka samun ce-ce-ku-ce a wajen nad'in wanda zai gaje ta. A 'karshe sai gwamnatin lokacin ta za'bi wanda ta ke ganin zai fi biya mata muradunta, ko kuma, kamar yadda ya faru a wannan karon, gwamna ya sakankawa wani wanda ya taimaka masa a siyasance da kujerar—ke nan ta zama tukwici.

Kowa ya san cewa lokacin da aka kafa garin Jos, babu wata sarauta mai suna ‘Gbong Gwom’. Turawa ne suka 'kir'kire ta da manufofi guda biyu. Manufa ta farko ita ce samar da kishiya ga masauratar da ke da iko a garin Jos a wancan lokacin—wadda suke tsoron tarin ikon da take da shi—da kuma, daga 'karshe, kashe ta d'ungurungum da maye gurbin ta da wadda suka 'kir'kira.

Manufar su ta biyu ita ce samar da wata masarauta wadda za ta ba su damar aiwatar da manufarsu ta mulkin mullukiyya (indirect rule), a lokaci guda kuma su cusa yankin a 'kar'kashin 'kabilun da ba Musulmi ba. A lokacin da aka 'kir'kiri sarautar, aka nemi wanda zai d'are gadonta daga cikin dagatan 'kauyukan da aka ambata a baya, aka rasa; dole aka je aka jaji'bo wani hedimasta mai suna Rwang Pam aka d'ora shi a kan kujerar. Sai dai daga su Turawan, har su wad'anda aka tilastawa hawa kujerar sarautar, babu wanda ya yi tunanin tsara yadda za a ri'ka gadon kujerar.

Wannan al’amari ya yi matu'kar dad'i ga Gwamnan Jihar Filato, Jonah David Jang, wanda tuni ya ke ta shirya yadda 'kauyen da ya fito, wato Du, zai zama zuciyar Jihar Filato. Ko da ya ke ya fahimci muhimmancin Jos, musamman 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa, a Jihar, don haka ba zai yiwu ya na'kasa Jos d'in gaba-d'aya ba, Jang ya yi dogon tunani, da taimakon ‘yan uwansa ‘yan Du, a kan yadda zasu samu damar kame duk madafun iko a Jihar.

Tuni Jang da abokansa, musamman tsohon Kwantulora Janar na Kwastam, kuma sabon Gbong Gwom, Jacob Buba Gyang, suka rarraba madafun ikon Jihar a tsakaninsu da ‘yan korensu. A rabon da aka yi, an baiwa 'kanin Buba Gyang, wato Timothy Buba Gyang, kujerar shugabancin 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa, shi kuma tsohon kwastam d'in aka ba shi kujerar Gbong Gwom (an yi wannan ne tun kafin mutuwar Victor Pam). Sannan kuma Jang yana nan yana ta 'ko'karin d'auke Gidan Gwamnati daga Ray Field ya mayar das hi Du (kai kuwa, ai da arzi'ki a garin wasu, gara a garinku, a garin naku ma gara a gidanku). An ce don wannan ha'ka ta cimma ruwa, Buba Gyang ya kashe miliyoyin nairori wajen ganin Jang ya zama gwamna.

Haka nan, saboda wannan rashin asali, shi ya sanya aka d'auki sarauta, wadda itace take nuna 'kima da darajar al’umma, aka dan'ka ta a hannun mutumin da Hukumar Ya'ki da Ma'kar'kashiya ga Tattalin Arzi'kin 'Kasa (EFCC) take tuhumarsa da yin almundahana, da had'a baki don a cuci al’ummar 'kasa. Ko kuma a cikin mutanen da suka nemi hawa sarautar babu mai gaskiya, ri'kon amana, dattako, yakana, da wadatar zuci ne, oho.

Wani abin mamaki shi ne, kamar yadda wani malamin tarihi a Jami’ar Bayero ta Kano yake fad'i, ta yaya za a yi kuna fad'a da mutane, kuna zaginsu, ba kwa son su, amma kuna han'koron samun masarautu irin nasu? Akwai lokacin da wani d'an gani-kashe-ni daga Yammacin Najeriya ya je Jos, ya ga suturun sarakai da manyan ‘yan siyasa irin na Hausawa, ya kuma ji duk Hausa suke yi, sai ya yi tir da su, ya kuma yi kiran su yi watsi da al’adun Hausawa. To amma idan wancan d'an gani-kashe-nin yana tunanin za su koma d'aura ganye ne, ya sha mamaki. Don kuwa koda yake Victor Pam ba ya d'aura rawani kamar yadda Fom Bot ya kasance ya na yi, sai dai ya sanya hula ha'bar-kada, har yanzu rigunan Hausawa su ke sanyawa sannan sarakansu na da sunaye irin na Huasawa: sakin fada, waziri, d’an masani, sardauna, da sauransu. Ko da yake idan ka ga sarakan, ba su da wata 'kima (na ta'ba zuwa fadar lokacin Fom Bot, da na ga Sarkin Fadansa na d'auka wani talaka ne ya zo neman na cefane).

Duk abin da ba a dasa shi a kan gaskiya ba, to babu inda za shi ko da kuwa za a yi ta ma'kurawa mutane shi don biyan bu'katun wasu tsirarun mutane. Haka nan kuma, Hausawa suna cewa “tsintacciyar mage ba ta mage”, don haka wannan sarauta ba za ta ta'ba yin tasirin da ake zaton za ta yi ba; wad'anda ke han'koron samun ta ma suna yi ne don su samu wata kafa ta yin girbi a inda ba su yi shuka ba. Kuma zalunci ba zai ta'ba d'orewa ba. Don haka 'karshen alewa 'kasa.

Saturday, February 07, 2009

Mu Ne Sauyin Da Muke Bu'kata

Babu shakka zai yi wuya a samu wani d'an Najeriya da ba ya kokawa a kan halin da 'kasar nan ta ke ciki. Haka nan kuma yake da wuya a samu wanda ko wad'anda suka yi imanin cewa akwai yiwuwar samun gyara balle har su yi tunanin yadda za a samar da wannan gyara. A 'kalla wannan shi ne abin da na fahimta daga irin zantawar da na yi da ’yan Najeriya da dama.

Wani abin ta’ajibi a irin wannan mahanga ta ’yan Najeriya shi ne yadda mutane za su yarda cewa lallai akwai sake a yadda al’amuransu suke tafiya, amma kuma a maimakon su yi yun'kurin kawo sauyi, sai su nad'e hannayensu, su koma gefe, su ce Allah Ya gyara, ko kuma su ce ba za a samu gyara ba. Wannan, a gani na, abin da a Turance za a iya kiran shi defeatist mentality ne—wato mutuwar zuciya. Wannan mutuwar zuciya kuma ita ta hana 'kasar ta kama hanyar gyara.

Kwanan baya na yi hira da wani d'an uwa wanda ya yi ta yabon d'aya daga cikin gwamnonin mu na Arewa. A cewarsa, wancan gwamna ya yi 'ko'kari matu'ka. Da na nemi jin abin da gwamnan ya yi, sai ya ce ai ya rarrabawa mutanen jiharsa kud'i. Ni kuwa sai na ka da baki na ce wannan ma gwaninta ce, amma kuma abin da gwamnan ya yi zai sanya zuciyar mutanen jihar ta mutu. Ina ma, na 'kara fad'ad'a jawabi na, gwamnan ya nunawa jama’ar jiharsa yadda za su kama kifi maimakon ya ri'ka basu shi a soye!

A nan ne wannan d'an uwa ya ce idan gwamnan bai yi haka ba (bai nunawa mutane yadda zasu kama kifi ba), to ba laifinsa ba ne; don kuwa akwai manoman da ya rabawa taraktocin noma don su bun'kasa sana’arsu ta noma amma sai suka sayar da taraktocin. 'Dan uwan ya 'kar'kare maganarsa da cewa 'kasar nan ba za ta gyaru ba, sai dai in har ba mu ne ke rayuwa a cikinta ba.

Da dad'ewa, tun kafin wannan tattaunawa da na yi da wannan d'an uwa, na ta'ba yin makamanciyar ta da wasu abokan aiki na lokacin da shugaban 'kasar Amurka na yanzu, Barack Obama, ya ci za'ben fid da gwani na jam’iyyar Democrat. Na shaidawa wad'annan abokan aikin nawa cewa nasarar da Obama ya samu za ta iya zama darasi garemu a fatan da muke yi na samun sauyi a 'kasar nan.

Masharhanta sun bayyana cewa Obama ya yi nasara ne ba don ya fi abokan karawarsa iya siyasa ko 'karfi ba. A cewarsu, tsabar zurfafa tunani da hangen nesa, sannan da amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da ma wad'anda ba na zamani ba, su suka taimakawa Obama. Misali, lokacin da ya yanke shawarar tsayawa takara, Obama ya yi zuzzurfan tunani a kan 'kalubalen da zai fuskanta, kasancewarsa “ba'kar fata”. Sannan ya duba ya ga cewa ba shi da 'karfin da zai iya yin nasara a fagen siyasar Amurka na al'ada.

Saboda haka ne Obama ya yi tunanin a maimakon ya yi ta ha'kilon shawo kan masu fad'a a ji a siyasar 'kasarsa, wad'anda ba za su taimaka masa ba, me zai hana ya fad'ad'a fagen ya shigo da sabbin maza'bu (masu za'be)? Nan ne fa Obama ya duba ya ga cewa matasan Amurka na bu'katar sauyi a fagen siyasar 'kasar; saboda haka ya tunkare su da sa'konsa na kawo sauyi, kuma suka amsa. A yanzu haka, al'kaluma sun nuna cewa akwai miliyoyin mutane a Amurka wad'anda ta hanyar Obama suka shiga siyasa. Sannan akwai miliyoyi da su ka yi aikin sa-kai don ganin an za'bi Obama, wad'anda ko bayan za'ben sun ci gaba da had'uwa don tattauna yadda za su ci gaba da yin tasiri a fagen siyasar 'kasar. Gaba d'aya wad'annan Obama ya kame zukatansu.

Bayan na kawo wannan dogon misali, sai na ce mu ma masu son ganin sauyi a Najeriya za mu iya zaburar da talakwa su yi wani gagarumin yun'kuri cikin ruwan sanyi, su sauya al’amura. Nan take abokan aiki na suka 'ke'kasa 'kasa suka ce sam hakan ba zai ta'ba yiwuwa a nan 'kasar ba. Babbar hujjar su ita ce Obama ya tara ma'kudan kud'ad'e don ya'kin neman za'be a Amurka; mutanen Najeriya talauci ya yi masu yawa don haka ko anini babu wanda zai iya bayarwa don za'ben wanda zai iya kawo sauyi a 'kasar. Mutane suna ta abin da za su ci ne, ko kuwa abin da za su bayar don yin wani abin da suke ganin ba za su amfana da shi kai tsaye ba?

Hujjar abokan aiki na ta biyu ita ce: Obama ya zaburar da wasu mutane da suka shiga aikin sa-kai don yad'a manufarsa. Wasu daga cikin wad'annan mutane ba su kar'bi ko sisi ba su ka ri'ka bi gida-gida suna jawo hankalin al’umma da su fito su yi rajista kuma su je su kad'a 'kuri’a ma Obama. A Najeriya, inji abokan aiki na, wanene zai iya sadaukar da lokacinsa don yin wannan? Babu.

Wad'annan hujjoji ne masu 'karfi. Kuma a ha'ki'kanin gaskiya, da ni ba mai 'karfin imani da abin da na yi imani da shi ba ne, da sun canja mani ra’ayi. Tuni! To amma ni ina ganin wad'annan kalamai na su su ma alama ce ta mutuwar zuciya.
Ta yaya za a samu sauyi idan wad'anda za su yi aikin samar da shi (kuma suke ta 'korafi kulliyaumin) suka kasance sun dasa zukatansu a kan cewa ba zai yiwu ba? Idan muka sake waiwayar sa'kon Obama, za mu ga cewa abin da ya gayawa magoya bayansa har ya samu nasarar jawo hankulansu shi ne: Yes, We Can! Ma’ana, Tabbas, Za Mu Iya!

Shi yasa jawabin 'karshe da na yiwa d'an uwan da na bud'e wannan ma'kala da labarinsa shi ne: “Kai ba abokin tafiya ba ne a gare ni domin ni na yi imanin cewa zan iya kawo gyara”. Gaskiya ne masu 'batawa sun fi masu son gyara yawa a 'kasar nan, nesa ba kusa ba. Kuma gaskiya ne cewa masu son a ci gaba da tafiya a karkace ba za su ta'ba yarda su ba masu son kawo gyara dama ba. Amma ni, a gani na, wannan ba dalili ba ne da zai sanya mu yi tagumi mu zuba ido mu ce babu abin da zai gyaru.

Abu d'aya ne ya sanya min wannan imani ya kuma 'karfafa shi a zuciyata. Wata rana na halarci wata lacca da Malam Umar Sani Fagge ya gabatar a Kano. A duk abubuwan da ya fad'a a fiye da awa d'aya da ya yi yana jawabi, wanda ya ma'kale a cikin zuciyata shi ne cewa aikin da annabawan Allah suka yi [na gyaran al’umma] tamkar mutum ne ya samu rafi yana gangarowa daga kan tsauni, ya ce zai mayar da shi ya haura.

To kuwa idan annabawa sun yi nasara a wannan aiki, babu abin da zai hana bayin Allah a ko wane zamani su yi nasara idan suka fawwala lamuransu ga Mad'aukakin Sarki, suka yi aiki tu'kuru. Za mu fahimci hakan idan muka tuna cewa Allah (SWT) Ya umarci ManzonSa Muhammad (SAW) da cewa: “Ka ce: ‘Wannan shi ne tafarki na; ina kira zuwa ga Allah a bisa basira, ni da duk wanda ya bi ni…’”. Mahallushshahid a nan shi ne kiran ba na Manzo ne shi kad'ai ba, a’a har ma da duk wanda ya bi shi. Sannan kuma Allah Ya yi al'kawari cewa zai bayar da nasara ga masu tsoronSa.

Abu na farko da muke bu'kata a wannan yun'kuri na gyaran al’amura shi ne, mu yi imani cewa Allah Yana tare da mu kuma Zai taimake mu. Kai idan ma muna ganin al’amarin ba na addini ba ne—yana da kyau mu tuna cewa Allah Ya tsarawa Musulmi rayuwarsa gaba d'ayanta—to wajibi ne mu yi imanin cewa tabbas za mu iya. A cikin littafin Baibul, an ruwaito cewa Annabi Isa (AS) ya ce imani zai iya matsar da tsauni daga inda ya ke.

Abu na biyu kuma da muke bu'kata shi ne, wajibi ne mu zama masu abin da bature yake kira positive thinking ko positive attitude. Ma’ana tunaninmu a ko yaushe ya zama na nasara ne ba na asara ba; d'abi’unmu su zama na masu kyakkyawan fata ba marasa fata ba. Wannan shi zai sanya a maimakon ko yaushe mu kasance muna tunanin girman matsala (girman kuma yana tsorata mu) sai mu ri'ka hararo maslaha. Shi ne kuma zai sanya mu ri'ka hangawa don hango abin da zai cutar da mu, mu yi saurin samo hanyar kawar da shi; da kuma abin da zai amfane mu mu hanzarta samo hanyar kusanto da shi.

Abu na uku shi ne, mu zamo sauyin da mu ke bu'kata. Misali, muna so mu ga ana yin adalci a 'kasar nan. To wajibi mu ri'ka yin adalci a junanmu. Kwanan baya muna hira da wani wanda tuni ya fara d'aukar matakan kawo gyara ta hanyar gyara kansa, sai yake ba ni labarin cewa sa'banin yadda direbobi a titunanmu ke 'ko'karin shigewa gaban ‘yan uwansu 'karfi da yaji, shi ya kan ha'kura idan ya tarar da motoci a gabansa har sai dama ta samu ya wuce. Sannan kuma ba ya sauka daga kan titi ya ra'be don isa dab da jankshan.

Wajibi ne idan muka zo muka samu ana bin layi, ko da kuwa na menene, mu yi ha'kuri mu bi har an zo kanmu a maimakon mu yi tsallake saboda akwai wani da muka sani da zai iya yi mana alfarma.

Haka nan kuma, wajibi ne ko wannenmu ya tashi ya nemi na kansa, kar ya zauna yana “Allah Ya ba ku mu samu”. Wani bawan Allah Ya ta'ba shaida min cewa shi a kan ya yi bara ko ro'ko, ya gwammace ya zauna da yunwa—kuma ya sha zama hakan har Allah, cikin IkonSa, Ya aiko masa da bud'i. Sannan kuma wajibi ne ko wannenmu ya ri'ke sana’arsa da kyau; ‘yan kasuwa a cikinmu su guji yin algush da tauye mudu da rantsuwa a kan 'karya; ma’aikata su yi aiki tsakani da Allah ba cuta ba cutarwa, ba aringizo ba ruf da ciki a kan dukiyar al’umma. Kuma mu kasance a ko yaushe muna neman hanyoyin inganta sana’o’inmu. Manzon Allah (SAW) ya ce Allah Ya wajabta kyautatawa a cikin dukkan al’amura; ma’ana duk abin da za mu yi to mu yi shi da kyau.

Haka nan kuma wajibi ne mu ri'ka sadaukar da kawunanmu don taimakawa bayin Allah duk sanda za mu iya, ko da kuwa da murmushi ne. Wata'kila ba za mu fahimci haka ba, amma murmushi shi ne mafi girman makami, gayawa-jini-na-wuce.

Bayan haka kuma dole ne mu zamo masu ha'kuri. Ha'kuri, inji Manzon Allah (SAW), haske ne. Hausawa kuma sun ce mai ha'kuri ya kan dafa dutse har ya sha romonsa. Na kan yi mamaki idan na ga mutane suna ha'ki'kicewa a kan abin da bai taka kara ya karya ba, duk su gajiyar da kawunansu a banza a wofi sannan daga 'karshe abin da suke so ya kasa samuwa.

Wad'annan abubuwa ba su ke nan ba. Amma idan mutum ya fara tunani mai kyau to zai ga wasu al’amura da yawa da zai iya gyara kansa da su, sannan yin hakan kuma ya sanya ya samu natsuwa da kwanciyar hankali.

Hausawa dai na cewa kowa ya daka rawar wani, to zai rasa turmin daka tasa.