Tuesday, May 21, 2013

Dokar ta-baci ta bar baya-da-kura

An sabunta: 16 ga Mayu, 2013 - An wallafa a 15:34 GMT

Tun bayan da Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ayyana dokar ta-baci a jihohin arewa guda uku, mutane daga sassa daban-daban na kasar ke tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan mataki. Yayin da wadansu ke yin na'am wadansu kuwa nuna rashin amincewa suke yi.

Jihohin da al'amarin ya shafa dai su ne Adamawa, da Borno, da Yobe.

A wani jawabi ne dai da ya yi ta gidan talabijin na kasa ranar Talata [14 ga watan Mayun 2013], Shugaba Jonathan ya ce bayan tuntubar juna, ya yanke shawarar yin "amfani da damar da Sashe na 305, karamin sashe na 1 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 wanda aka yi wa gyara ya ba ni, na ayyana Dokar ta-Baci...".

Ya kuma ce hakan ya zama wajibi ne saboda "yaduwar ayyukan 'yan ta'adda, da kuma kalubalen tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a wadansu sassan kasar, musamman ma a [jihohin] Borno, da Yobe, da Adamawa, da Gombe, da Bauchi, da Kano, da Filato, da kuma na baya-bayan nan, Bayelsa, da Taraba, da Benue, da Nasarawa".

Tuni an kaddamar da hari

Tuni ma dai, kamar yadda wata majiya ta soji ta bayyana, sojoji suka fara kaddamar da hare-hare da nufin kawar da 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad--wacce aka fi sani da suna Boko Haram—a gandun dajin Sambisa da ke jihar Borno ranar Laraba.

Majiyar ta kuma ce sojoji dubu biyu aka tura jihar ta Borno, ko da yake ba a bayyana ko nawa aka tura sauran jihohin biyu ba.

Tun kafin ayyana dokar dai, kungiyar gwamnonin kasar ta fitar da wata sanarwa mai dauke da sa-hannun shugabanta, Gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Rivers, tana bayyana rashin amincewa da matakin.

Sai dai kuma jim kadan da ayyana dokar, gwamnatin Jihar Yobe—daya daga jihohin da abin ya shafa—ta hannun mai baiwa Gwamna Ibrahim Gaidam shawara a kan al'amuran yada labarai da 'yan jarida, Abdullahi Bego, ta goyi bayan matakin.

Gwamnatin Yobe ta goyi baya

A wata sanarwa da ya fitar sa'o'i kalilan bayan jawabin Mista Jonathan, Malam Bego ya bayyana cewa, "Kamar yadda kowa ya sani, babu abin da ya fi zaman lafiya. Don haka ne Gwamnatin Jihar Yobe ta amince da Shugaban Kasa a kan bukatar daukar karin matakai don magance matsalar tsaro a kasar nan...". Mai yiwuwa gwamnatin Jihar ta Yobe, da ma sauran gwamnatoci, sun sauya shawara dangane da dokar ta-bacin ne saboda—kamar yadda sanarwar mai dauke da sa-hannun Malam Bego ke cewa—"ayyana dokar ta-bacin da Shugaban Kasa ya yi ba ta shafi [masu rike da] mukaman siyasa a jihar ba...".

Sai dai kuma kungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) ta al'ummar Musulmin Najeriya ba ta goyi bayan ayyana dokar ba saboda a cewar Sakatarenta na kasa, Shaikh Dokta Khalid Aliyu Abubakar, "ba a gama warkewa daga raunin matsalar Baga ba, aka zo ta Bama...inda ma fa ba a ce dokar ta-baci ba ce ga abubuwan da su ka faru na aika-aika...".

JNI ta nuna damuwa

Ga alama, damuwar da JNI ke nunawa ita ce inda ba a ayyana dokar ta-baci, an baiwa jami'an tsaro dama su ci karensu ba babbaka ba ma, an yi kashe-kashe, balle kuma inda aka kara jibge sojoji.

Wannan ra'ayi na JNI dai ya yi hannun riga da na Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), wacce ta ce a ganinta da ma matakin da ya kamata a dauka ke nan tun tuni.

A cewar Sakataren CAN din na kasa, Reverend Asake, "kamata ya yi ma da an [kafa dokar] tun tuni, da an ceci rayuka. Amma kuma muna fata, muna kuma addu'a Allah Ya sa wannan zai biya bukata a daina [kashe-kashe]".

Wadansu masana harkar tsaro ma sun bayyana fargabar cewa kara yawan sojoji zai iya kara haddasa keta hakkokin bil-Adama.

Dokta Bawa Wase wani mai nazari a kan al'amuran tsaro a kasar ta Najeriya; yana cikin masu irin wannan ra'ayi.

Tasirin dokar

"Tasirin da [aikewa da karin sojoji zai yi", inji Dokta Wase, "shi ne zai dada ruda al'amarin--za a keta hakkin dan-Adam; za kuma a shiga yin mugunta; za a shiga yin kisa na ba gaira ba dalili; zai kuma tayar da kaimi na matasa da al'umma na bangaren da abin ya shafa...".

Su dai masu goyon bayan ayyana dokar ta-bacin, musamman ma kungiyar CAN, suna ganin lokaci ya yi da ya kamata a soke kwamitin nan da gwamnatin kasar ta kafa don ya lalubo hanyoyin sasantawa da 'ya'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal-Jihad.

Ko da yake ita kungiyar CAN da ma can ba ta goyi bayan tayin afuwa ga 'yan kugiyar da sasantawa da su ba, wadansu 'yan Najeriyar gani su ke cewa da ma can abin da gwamnatin ta yi niyyar yi ke nan: wato kafa dokar ta-baci.

Dokta Abubakar Kari, malamin Kimiyyar Siyasar Zamantakewa a Jami'ar Abuja, yana cikin masu irin wannan ra'ayi: "Wannan mataki da aka dauka bai zo da mamaki ba, mai yiwuwa saboda dalilai biyu ko uku: na farko dai kusan mako daya ke nan ake ta rade-radin cewa gwamnati za ta dauki wannan mataki; na biyu kuma ina ga tun lokacin da wani [dan Majalisar Dattawa] daga Jihar Borno ya fito fili ya ce kusan kashi tamanin cikin dari na sassan jihar yana hannun masu tayar da kayar baya, muka fara tunanin cewa lallai gwamnati za ta dauki mataki; na uku kuma, wasunmu suna ganin cewa da ma tun tuni irin wannan mataki shi ne wanda Shugaba Goodluck Jonathan da mukarrabansa suke so su dauka, amma ba maganar tattaunawa ba".

Makomar kwamitin sasantawa

Sai dai kuma mai baiwa shugaban kasar shawara na musamman a kan hulda da jama'a, Dokta Doyin Okupe, ya ce sam gwamnati ba ta da niyyar rushe kwamitin lalubo hanyoyin sasantawar. A wata hira da ya yi da BBC, Dokta Okupe ya ce; "Aikin kwamitin da kuma sanarwar kafa dokar ta-baci abubuwa biyu ne mabambanta—aikin kwamitin shi ne nemo hanyoyin samun zaman lafiya da kuma hanyoyin tattaunawa tsakanin gwamnati da mambobin kungiyar ta Boko Haram wadanda ke so a yi sulhu.... Ke nan maganar soke kwamitin ba ta ma taso ba".

Wadansu 'yan Najeriyar kuma cewa suke yi akwai siyasa a wannan al'amari; amma a cewar Dokta Kari, ko da an yi irin wannan tunani—kasancewa jam'iyyar adawa ta ANPP ce ke mulki a jihohin Borno da Yobe, kuma ba a jituwa tsakanin shugaban jam'iyyar PDP mai mulki wanda ke samun goyon bayan shugaban kasa da gwamnan Jihar Adamawa—babu gwamnatin da za ta ga abin da ke faruwa a kasar ba ta dauki kwakkwaran mataki ba.

A halin da ake ciki dai mazauna jihohin sun bayar da labarin ganin karin sojoji a yankunansu. Amma babban abin da ke daurewa 'yan Najeriya da dama kai dai shi ne ta yaya gwamnati za ta ce tana neman yin sulhu da wadanda take kira masu tayar da kayar baya a gefe guda sannan kuma a daya gefen ta kafa dokar ta-baci ta baiwa dakarunta umarnin yin duk abin da suka ga ya dace don murkushe su?

Daga BBC Hausa