Monday, December 01, 2008

Hannuwan Jang Sun Yi Jina-jina

Zai yi wuya a ce, ya zuwa yanzu, akwai wanda bai samu labarin hatsaniyar da ta hargitsa garin Jos ba, inda aka kashe d'aruruwan mutane, mafi yawancinsu da harsashin 'yan sanda. Wasu mutanen da aka kashe ma ba mazauna garin Jos ba ne, wucewa kawai su ka je yi. Haka kuma zai yi wuya a ce akwai wanda bai ji irin zarge-zargen da mahukunta a Jihar Filato su ke ta yi ba—cewa wannan yamutsi shirya shi aka yi don hana garin, da ma Jihar, zaman lafiya.
Babu shakka, za mu iya yarda ba tare da wata-wata ba, cewa wannan aika-aika an dad'e da shirya aikata ta. Sai dai abin tambaya shi ne, su wanene su ka shirya ta? Don amsa wannan tambaya muna bu'katar yin wasu 'karin tambayoyi ko ma iya fahimtar al’amarin a muhallin da ya dace.
Da farko, su wanene su ka fito fili su ka ce tun da a wasu jihohi jam’iyyar da ke mulki ce ta lashe za'ben dukkan 'kananan hukumomi, wajibi ne a Jihar Filato ma hakan ta kasance, ko da kuwa sama da 'kasa za su had'u? Sannan su wanene su ka fito fili su ka ce ba za su sake yarda wani mutum daga wata al’umma ya sake mulki a 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa ba, ko da kuwa wannan al’ummar ita ke da rinjaye? Bayan wannan su wanene suka d'auke wurin tattara sakamakon za'be daga Sakatariyar 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa, inda a nan ne aka saba tattarawa, su ka mayar can bayan gari, ihun-ka-banza (don su samu sakewa su yi magud'i yadda su ke so)? Su wanene su ka lashi takobin 'kwace garin Jos 'karfi da yaji don su samu damar cin zarafin wata al’umma wadda da jininta da guminta aka kafa garin har ya bun'kasa ya kai inda ya kai yanzu?
Kafin mai karatu ya amsa wad'annan tambayoyi, ga wani bayani kad'an game da mutumin da a halin yanzu ya ke ri'ke da ragamar gwamnatin Jihar Filato (a 'kar'kashin kulawarsa komai ya faru), wanda a ko yaushe ya ke tutiyar cewa yana son Jihar ta zauna lafiya. Wad'anda suka san Jonah David Jang sun ce shi Kirista ne irin wad'anda su ke kiran kansu born again (in ka so ka ce ‘yan gani-kashe-nin Kiristanci). Wannan tsatstsauran ra’ayin Kiristancin ne ya sa bayan ya hau mulki ya haramtawa mata masu nuna tsiraicinsu shiga gidan gwamnati da ma sakatariyar gwamnatin Jihar. Ko da ya ke an ce kasancewarsa born again ta sa ba ya shan barasa, amma idan ka dubi idanuwansa da kyau za ka ga alamar a da ya d'an ta'ba.
Wani abu da ya kamata mu fahimta da Jang shi ne cewa shi fa ba kamar sauran 'yan siyasa ba ne. A baki duk wani d'an siyasa ya kan ce yana neman mulki ne don yi wa talaka aiki; a aikace kuma yana yi ne don cika aljihunsa kawai. To amma shi Jang babban ginshi'kin siyasarsa shi ne 'kiyayya ga Musulmi, musamman Hausawa, da addininsu na Musulunci. Cin zarafinsu kuma shi ne manufarsa ta neman mulki. 'Kasa kad'an da wannan manufa kuma akwai burin ganin ya 'kwato duk wasu madafin iko a Jihar Filato ya dan'ka a hannun 'yan 'kabilarsa ta Birom, wad'anda kafin shi ba su ta'ba samu an za'bi wani daga cikinsu ya hau kujerar gwamnan Jihar ba (duk da i'kirarin da suke yi cewa sun fi ko wacce 'kabila yawan mutane a Jihar). Wannan ne ya sa yayin da sauran 'yan siyasa su kan tauna su kuma ciza magana kafin su furta, shi Jang ko yaya ta zo furzarwa ya ke—komai munin ta.
Wasu majiyoyi sun ruwaito cewa a lokacin da yake neman tsayawa takarar gwamna, al’ummar Musulmi sun nemi ya za'bo mataimaki Musulmi don su goya masa baya. Shi kuwa sai ya ka da baki ya ce shi bai ga dalilin da zai sa ya d'auki mataimaki Musulmi ba, don kuwa yana ganin Musulmi ba su da wani tasiri ko muhimmanci a tsarin rayuwar Jihar Filato: ma’ana, da su da babu su duk d'aya ne a wurinsa, kai idan akwai yadda zai yi ya kawar da su ma zai yi. Mutanen Jihar Adamawa, inda ya ta'ba yin Gwamnan mulkin soja, ma sun shaidar da cewa ba ya 'kaunar Musulunci da Musulmi.
Bayan wannan, tun bayan hawansa gadon mulki a Jihar Filato, Jang ya ke ta d'aukar matakai da za su iya yin karen-tsaye ga gurguntaccen zaman lafiyar da yake wanzuwa a Jos tun bayan rikicin 2001. Misali, jajircewar da ya yi sai ya d'auke Sakatariyar 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa daga inda ta ke ya kai ta inda 'yan 'kabilarsa ta Birom su ka yi dafifi, duk kuwa da cewa wancan wurin yana da nisa daga cibiyar garin Jos, kuma su 'yan 'kabilar tasa ba su taka kara sun karya ba a 'karamar hukumar. Sannan kuma ya nace sai ya fad'ad'a fadar Gbong Gwom Jos, ya gina masa majami'a, duk kuwa da cewa shi Sarkin Birom d'in bai ta'ba kwana a fadar ba. Kai ko Fom Bot ma bai ta'ba kwana a fadar ba, balle Victor Pam.
Idan ba a manta ba, a za'ben da ya soke kwanan baya, Jang ya d'auki duk wasu matakai da ya ke ganin za su bashi dama ya d'ora d'an uwansa a kan karagar shugabancin 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa amma bai yi nasara ba. Don haka a wannan karon, kamar yadda wasu majiyoyi su ka ruwaito, ya 'kalubalanci wasu 'yan barandansa daga cikin al’ummar garin Jos da ko da yaya su tabbata su kawo masa 'karamar hukumar. Wad'annan 'yan barandan nasa su ne su ka d'auki nauyin wasu zauna-gari banza, da kuma 'yan bunburutu don su ri'ka kafewa da kuma gadin fastocin d'an takarar Jang a cikin garin Jos. Sannan kuma, kamar yadda wad'nnan majiyoyi su ka ruwaito, aka umarci wad'annan tsagera su tayar da yamutsi idan su ka ga d'an takarar Jang ba zai yi nasara ba.
Bayan Jang ya haddasa zanga-zanga, nan da nan ya umurci 'yan sanda su bud'e wuta a kan duk wanda su ka gani. Abin mamaki shine duk da cewa mutanen Jos gaba d'aya sun shige cikin gidajensu bayan jin wannan umurni da aka bayar ga 'yan sanda, sai ga 'yan sandan kwantar (wad'annan tayarwa su ka yi ta yi) da tarzoma suna bi gida gida suna fasa 'kofa su na kashe bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba. Wasu ma na cewa 'yan CAN (wato 'Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya) ne sanye da kayan 'yan sanda ke kashe mutane—in ma hakan ne to ba abin mamaki ne, don tun farkon shekarun 1990 jaridar The Pen, wacce ta dad'e da kwanta dama, ta ruwaito cewa 'kungiyar na ta tara muggan makamai don kai hari a kan Musulmi.
Sannan kuma Gwamnatin ta bayar da labarai ga kafofin yad'a labarai na kudancin Nijeriya mai nuna cewa al’ummar Musulmi ne su ka ri'ka kashe mutane. Ka ga ke nan an cuci mutane an kuma d'ora masu laifi. Ga wanda bai sani ba, wakilan wad'annan kafofin watsa labarai na kudu a zaune su ke ko yaushe a gidan gwamnati, idan labari ya zo su kar'ba a biya su su aika don jaridunsu su buga. Na ma ta'ba zuwa wani gidan gwamnati inda na ga irin wad'annan 'yan jarida suna fad'a a wajen rabon irin kud'in da ake ba su. Shi yasa duk jaridar da ka karanta sai ka ga labarin ya sa'ba da ha'ki'kanin abin da yake faruwa — me zai hana kuwa, tun da labarin daga Nuhu Gagara aka samo shi?
Babu shakka Jang shi ke da alhakin kashe d'aruruwan mutane a Jos saboda tsabar 'kiyayya da kafiya a kan abin da bai dace ba — abin da mai hankali da tunani da hangen nesa ba zai yi ba. Idan burin Jang da sauran ma'kiya Allah shi ne su kawar da Musulmi a garin Jos, to fa ya kamata su san cewa ba za su iya aiwatar da abin da Allah bai yi ba. Sannan kuma ya kamata su fahimci cewa akwai ranar 'kin dillanci.
Kuma yana da kyau Jang ya gane cewa idan har ya dage a kan aiwatar da wad'annan munanan manufofi nasa, to zai kai garin Jos da ma Jihar Filato ya baro ne kawai. Ga misali nan wad'anda su ka san garin Langtang suna bayarwa: rikicin da ya hautsina garin ya mayar da shi kangon garin da aka sani a da. To ko da su Jang sun samu damar kashe dukkan Musulmin da ke Jos, to fa garin ba zai ta'ba farfad'owa har su su ji dad'in zama a cikinsa ba.
Dangane da tunaninsa na cewa Musulmi ba su da tasiri kuwa, ya kamata ya tuna da 'kauracewa harkokin da al’ummar Jos su ka yi wanda ya tsayar da dukkan al’amura a garin. Wannan yana nuna cewa muddin al’umma ta 'kauracewa garin to ya mutu ke nan murus.
Su kuwa al’ummar garin Jos, ya kamata su san cewa lokaci ya yi da ya kamata su koma su sake shiri. Abin nufi a nan shi ne su sake tsarin tafiya. Babu shakka al’umma, musamman shugabanni, yanzu sun gane kurensu, musamman wajen za'ben d'an majalisar Jiha mai wakiltar Jos ta Arewa wanda ba shi da hadafi, bai san ciwon kansa ba. Kuma lokaci ya yi da ya kamata a had'a kai a fara d'aukar tsauraran matakai a kan mutanen da ake had'a baki da su don a cutar da al’umma. Me zai hana a sanyawa irin wad'annan mutanen irin takunkumin da aka sanyawa sahabban da su ka 'ki fita ya'ki a zamanin Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi)?
Ita kuma Gwamnati, musamman ta tarayya, wajibi ta yi bincike don gano musabbabin wannan rikici, ta kuma hukunta duk wanda aka same shi da laifi. Hukuncin kuma kar ya tsaya a kan wand'anda su ka d'auki makamai kawai, wajibi ne ya had'a har da wad'anda suka bayar da umarni da baki, da wad'anda su ka shirya magud'i. Kai ire-iren maganganun da ke fitowa daga bakin wad'annan mutane ma ya kai a d'auke shi a matsayin cin amanar 'kasa. Misali, wanne sashe ne na Kundin Tsarin Mulkin Najaeriya ya ce sai 'yan wata 'kabila ko addini ne kawai za su shugabanci wata 'karamar hukuma; har ta kai ga tsara yadda za a karkashe mutane don cimma wannan buri?
Allah Ya ji'kan Musulmin da suka rasa rayukansu a wannan aika-aika da Jang ya aikata; shi kuma Allah Ya nuna masa iyakarsa. Allah Ya taimaki Musulunci da Musulmi, amin.

Saturday, November 15, 2008

Bafulatanin Yola Ya Doke Hausawa a Gasar Adabin Hausa


Wani Bafillace daga Yola ta Jihar Adamawa ya doke Hausawa a gasar Adabin Hausa inda ya lashe kyautar lnjniya Muhammad Bashir 'Karaye kan Adabin Hausa ta bana (2008).
Littattafai 15 ne suka shiga wannan gasa, wad'anda shida daga cikinsu suka tsallake sirad'i na farko.
Wad'annan litlattafai shida su ne: Halin Rayuwa na Aliyu Z. Mainasara, da Kowa Ya Bi na Abdurrashid Sani Isa Nijeriya, da kuma Baki Abin Magana na Dala'ilu Bobboji. Sauran su ne littafin Ibrahim Birniwa mai suna Garinmu Da Nisa, da na Muhammad Lawal Barista, Ba'kin Kishi, da kuma na Nazir Adam mai suna Murmushin Alkawali.
Zakarun gasar su ne Dala'ilu Bobboji, mai littafin Baki Abin Magana, wanda ya yi na d'aya; da Ibrahim Birniwa, mai Garinmu Da Nisa, wanda ya yi na biyu; sai kuma Muhammad Lawal Barista, marubucin Ba'kin Kishi.
Zakaran gasar ta bana, Dala'ilu Bobboji, ya bayyana cewa ya rubuta Baki Abin Magana ne saboda takaicin da ya jima yana yi, ganin yadda littattafan Hausa suka zamo tamkar jarida.
"In ka d'auki littafi—abin mamaki—kana karanta shi kamar kana karanta jarida. Sai ka rasa inda aka faro labarin, ka rasa inda aka nufa, ka rasa kuma 'karshensa. Labarin ne za ka karanta ba ma'ana: daga soyayya sai soyayya; babu wani abin da zai burge ka sai soyayya kawai. Ni ma littafina akwai soyayya, amma na tsara shi ne da tsari, kuma yadda al'adar Bahaushe take", inji Malam Dala'ilu.
Marubucin ya kuma 'kara da cewa yadda ake d'aukar al'adun waje ana 'ko'karin 'ka'kaba su a cikin na Hausa da 'karfi da yaji abin takaici ne. “Shi ya sa na ce me zai hana na zauna na rubuta littafi irin na wad'anda suka yi na baya, domin da ka dauki littafi irin nasu kana karantawa, in dai kai makarancin Hausa ne, to za ka san ba ka 'ketare iyakar al'adarmu kamar yadda na zamani suke yi ba", inji Malam Dala'ilu.
Shi dai littafin Baki Abin Magana, an rubuta shi ne a bisa irin salon littafin Abubakar Imam, Magana Jari Ce, wanda d'aya ne daga cikin littattafan adabin Hausa mafi shahara, kuma d'aya ne daga cikin littafai uku da malamin ya rubuta a shekarar 1986 don shiga wata gasar rubutun adabi. Ya kuma rubuta wad'annan littattafai ne cikin wata bakwai.
An haifi Dala'ilu Bobboji a garin Song na Jihar Adamawa a shekarar 1966. Ya halarci Kwalejin Je-ka-ka-dawo ta Gwamnati da ke Yola (Yola Government Day College) da kuma Kwalejin Nazarin Shari'a ta Yola (Collegc of Legal Studies, Yola), inda ya fita da difloma kan Shari'a da Dokokin Zamani (Shari'ah and Civil Law).
Bayan kammala karantunsa, Malam Dala'ilu ya yi aiki a Kotun Daukaka Kara ta Shari'ar Musulunci da ke Yola, kafin ya koma Kwalejin Nazarin Shari'a, inda ya yi aikin karantarwa.
Ita dai wannan kyauta ta Adabin Hausa ta 'Karaye, matar marigayi Injiniya Muhammad Bashir 'Karaye, Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, ce ta assasa ta bara don 'kara 'kwarin gwiwa ga marubuta wajen rubutu a cikin harsunanmu na gida. Wanda ya zo na d'aya a gasar ya samu tsabar kud'i Naira dubu 150; wad'anda suka zo na biyu da na uku kuma sun samu Naira dubu 100 da Naira dubu 50.
'Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) da had'in gwiwar Gidauniyar Injiniya Muhammad Bashir 'Karaye suka d'auki nauyin shiryawa, tantancewa, da kuma bayar da wannan kyauta.
Daga cikin manyan ba'kin da suka halarci wajen bayar da kyaututtukan a Abuja har da tsohon ministan ma'adanai, Alhaji Bashir 'Dalhatu, da tsohon Babban Mai Shari'a na Nijeriya, Mai Shari'a Muhammad Lawal Uwais, da shugaban 'Kungiyar Marubuta ta 'Kasa kuma tsohon d'an Majalisar Wakilai, Dakta Wale Okediran da kuma wani malami a sashen Nazarin Harshen Ingilishi a Jami'ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Dakta E.E. Sule.
Wad'anda suka yi al'kalanci da tantance littattafan da suka cancanci yabo su ne Babban Daraktan Hukumar Talabijin ta Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Dachia da kuma Malam Kabir 'Dan'asabe, malami a Sashen Nazarin Harshen Hausa a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Zuba, Abuja.

Daga jaridar Aminiya, 3-9/11/1429 (31/10-6/11/2008)

Monday, June 16, 2008

Ingiza Mai Kantu Ruwa

Kwanan baya na hau bas zan tafi ofis. Da yake a wurin tsayawar ‘yan bas d'in na hau, sai da motar ta cika sannan muka tashi. Cikar kuma har ta batse, domin kuwa yaron mota a kan inji (maneji) ya ke.
A bisa al’ada, ‘yan bas sukan d'ebi mutane su ma'kare bas d'in: na ma ta'ba jin wani kwandasta (conductor) yana cewa ‘mota roba ce, ba ta cika’. Amma a Abuja yin hakan had'ari ne domin idan jami’an duba lafiyar motoci (VIO) su ka yi ido hud'u da direban da ya cika mota ya d'ora kwandasta a kan injin to sai ya yi ta wasu kud'ad'e masu d'an kauri—sai ya yi asara na ke nufi. Ga VIO kuma ba kamar ‘yan sanda ba; ba sa kar'bar na goro su 'kyale mutum.
Muna cikin tafiya sai ga motar VIO kamar daga sama! Muna isowa jankshan aka yi rashin sa’a jami’i mai bayar da hannu ya tsayar da motoci kuma babu yadda za a yi direban bas d'in nan ya juya ko ya canja hanya don ya tsere. Jami’an VIO suka yi masa nuni ya tsaya, amma wasu fasinjoji da ke motar, musamman wasu ‘yan mata su biyu, su ka ba shi shawarar kar ya tsaya. Lokacin da aka saki hanya, direban VIO ya nunawa direban bas ya fi shi iya mota don kuwa ya sha kansa ya hana shi guduwa.
Da direban bas ya ga ba sarki sai Allah, sai ya tsaya. 'Daya daga cikin jami’an VIO ya fito, sai muka ga dattijo ne; ga alama ya haura shekara sittin. Nan fa ‘yan matan nan da suka zuga direban bas suka yiwa wannan dattijo ca, suna cewa “Tsoho da kai ka zo kana neman cin-hanci. Me zai hana ka yi ritaya ka koma 'kauyen ku ka yi noma? Ire-irenka, tsoffin da suka 'ki yin ritaya, ku ne ku ka hana mu samun aiki”. 'Daya daga cikin ‘yan matan ta d'aga wani 'katon ambulan da ke hannunta ta 'kara da cewa, “Dubi takarduna, na gaji da yawon neman aiki ban samu ba saboda tsoho da kai ka 'ki ka yi ritaya a samu gurbin da za a d'auke ni”.
Alamu kuma sun nuna cewa d'aya jami’in ya fi wannan dattijon a mu'kami duk da shi matashi ne. Kuma ga alama ya yi tunanin tausayawa direban ya 'kyale shi, amma sai dattijon ya shaida masa abin da ‘yan matan suke fad'a; don haka jami’in ya canja shawara.
Daga 'karshe dai, ba girma ba arzi'ki, jami’an VIO su ka tilasta fasinjoji sauka daga mota domin a cewarsu za su tafi da direban nan ofishinsu ya je ya yi bayani. Shi kuwa kwandasta, tilas ya zaro kud'aden jama’a ya dan'kawa kowa abin da zai 'karasa da shi inda ya yi niyyar zuwa.
Had'ama ta sa direban bas ya yi asara goma da goma: zai yi asarar kud'ad'en da ya tara a wannan yini, ga shi kuma kud'in da ya kar'ba a hannun fasinjojin da su ka zuga shi ya 'ki tsawa dole ya mayar masu da abinsu; bugu da 'kari, fatan samun wasu kud'ad'en a wannan yinin yana dab da yankewa a zuciyarsa kwata-kwata, domin idan jami'an nan suka tafi da shi to sai abin da hali ya yi, ma'ana sai sanda aka ganshi. Mu ma ko ba komai an 'bata mana lokaci, sannan an sanya mu dole mu hau wata motar wadda da 'kyar mu ka samu.
Babu shakka masu cewa “A bi doka a zauna lafiya” sun yi gaskiya. Sannan kuma duk wanda ya biyewa mata, idan bai yi a hankali ba, to sai ya yi da-na-sani (ba ina nufin duk mata haka su ke ba; sai dai yana da kyau a ri'ka sara ana duban bakin gatari).
Ita kuma hukuma, wajibi ne ta tashi tsaye don gyaran tattalin arzi'kin 'kasa, domin talauci na d'aya daga cikin dalilan da suka sa mutane ke karya doka a 'ko'karin neman kud'i ta ko wacce irin hanya. Bugu da 'kari, hakan zai sa aikin yi ya samu, a rage yawan matasa masu zaman banza, da wad'anda suka galabaita wajen neman aiki har suka fara shiga wani hali da suka fara daina ganin kowa da gashi. Idan ba a yi hankali ba ma, daga nan sai su fara kai duka, ko ma abin da fi haka. Allah Ya sawwa'ke.

Saturday, May 17, 2008

"Mun 'Daura 'Damarar Ya'ki Da Jahilci Da Zaman Banza"


Daga Muhammad K. Muhammad
Alhaji Lawan Alhassan Mai Warwaro shi ne shugaban ri'ko na 'kungiyar Ibrahim Katsina Foundation (wato 'Kungiyar Raya Unguwar Ibrahim Katsina) da ke 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa. A wannan hirar da ya yi da Aminiya ya bayyana manufofin kafa 'kungiyar da kuma nasarorin da ta samu ya zuwa yanzu.
Aminiya: Menene ma'kasudin kafa wannan 'kungiya ta Ibrahim Katsina Foundation?
Alhaji Lawan: Dalilan da suka sa muka taru muka yi tunanin kafa wannan 'kungiya suna da dama 'kwarai. Kai da kan ka in ka lura [za ka ga] kullum duniyar ta mu 'kara ci gaba ta ke yi. Kuma ci gaba ba ya yiwuwa sai da al’umma; kuma ba ya yiwuwa da al’ummar sai an had'a kai. Duk sanda al’umma ta had'a kai, to za ta ci nasara a kan dukkan abin da ta sa a gaban ta. Amma daga lokacin da aka samu al’umma a d'aid'aikun su a warwatse, to karya su ba shi da wahala.
In ka lura, mu al’ummar mu ba mu saba da irin wad'annan 'kungiyoyi ba. 'Yan uwan mu da suke kudu ko yamma sun dad'e suna irin wad'annan tafiyoyin. Amma kuma daga lokacin da muka fara zuwa yanzu, mun yi 'karfin da 'kungiyoyin da suka shekara 50 ma ba su yi ba.
Aminiya: Ko za ka iya fad'a mana kad'an daga cikin manufofin wannan 'kungiya?
Alhaji Lawan: Manufar wannan 'kungiya ita ce: 'karfafa al’umma a kan al’amura, kamar ta wajen ilimi, ayyukan yi, dogaro da kai, wayar wa da mutane kai su san cewa su mutane ne—su san ’yancin kan su, zaman lafiya, da sauransu.
Aminiya: To wad'anne irin nasarori ku ka samu daga lokacin da aka kafa wannan 'kungiyar zuwa yanzu?
Alhaji Lawan: Alhamdulillahi, mun samu nasarori da dama. Na d'aya daga cikin abubuwan da muka fara yi, mun fara duba menene ya kan sa al’umma ta ci baya ko ta kasa ci gaba? Sai muka gane jahilci ne. Idan babu ilimi babu inda za a je. To sai muka ce mu fara d'aukar maganar ilimi mu sa a gaban mu. Sai muka duba al’ummar don mu ga ta ina ne za mu fara taimakawa ta 'bangaren ilimi? Sai muka ga akwai yara 'kanana wad'anda ba su zuwa makaranta, suna nan sai zaman banza, sai yawace-yawace. Sai muka kafa kwamiti mu ka ce ya binciko mana irin wad'annan yara, musamman marayu, da wad'anda iyayen su ba su da hali, amma suna da basirar karatu. Mu ka samu sunaye da dama daga ko wanne 'bangare na wannan maza'ba.
A wancan lokacin mun fara da yara kamar guda 40; muka sa su a firamare, muka biya masu kud'in makaranta, muka d'inka masu kayan makaranta, muka saya masu littattafai, kuma muka kafa kwamitin sa-ido (monitoring team) wanda ya ke zuwa makarantun nan ya tabbatar yaran nan suna zuwa kuma suna yin abin da ya kamata. 'Bangare na farko ke nan.
'Bangare na biyu shi ne sakandare. A wannan 'bangaren mun duba mun ga akwai yaran mu da yawa da suka gama firamare; su ma suna da bu'katar ci gaba amma babu hali. Muka taru muka yi doguwar shawara, muka ce akwai makarantu na ’yan uwa da abokan arzi'ki a gari wad'anda idan muka je muka ro'ki alfarma za a yi mana; saboda haka sai muka fara da makarantar uban mu, Alhaji Barau Abdullahi, mai suna Al-Hilal. Allah Ya taimake mu muka samu gurbin yara 10, wad'anda aka ba su daga 'karamin aji na d'aya (JSS1) har zuwa babban aji na uku (SSS3). Wato ba abin da za a biya a makarantar nan—su gudummawar su ga wannan 'kungiya ke nan.
Daga nan kuma sai muka tafi wata makaranta da ake kiran ta Trust International, ta Alhaji Tijjani Abdullahi. Nan ma—ko da yake ya ce shi ma akwai yaran marayu da ya ke taimaka wa da dama, amma tun da manufar mu ta alheri ce—ya ba mu [gurbin] mutum biyu.
Daga nan kuma sai muka tafi wajen wani d'an uwan mu Alhaji Hamisu Umaru, shi ma yana da makaranta mai suna Al-Haqq. Shi ma ya ba mu gurabe biyu. Sai kuma wani d'an uwan mu, Malam Idi Abubakar, yana da makaranta mai suna Al-Ikhlas. Shi ma ya yi mana alfarma, ya ba mu gurabe biyu. Dukka wad'annan su na nan a makarantun suna karatu.
Bayan waxannan kuma akwai wad'anda mu ke ta bi da dama, suka ga lokaci ya 'kure; amma bayan zangon karatu na ukun nan (third term), in Allah Ya yarda za mu samu gurabe da dama da za mu 'kara tura yara. Sannan a makarantun gwamnati ma muna nan muna 'ko'karin mu sa yara kamar guda 40. Mun tura ana ta yi mana 'ko'karin sama masu admission. Wannan 'kungiya ce za ta nemo kud'i ta biya masu kud'in makaranta, ta d'inka masu kayan makaranta, ta saya masu littattafai. Mu dai burin mu mu ga mun kawar da zaman banza, da jahilci da yaran mu ke yi.
Sannan muna da kusan mutm 50 masu bu'katar yin digiri. To suma mun bi jami’o’i kamar guda uku muna 'ko'karin cusa su. Sannan muna da wani uba, Malam Musa Muhammad, Limamin Abuja, shi ma ya d'ebi yara uku ya ba su tallafin karatu (scholarship) daga sakandare har zuwa jami’a—banda wad'anda na yi bayaninsu—Allah Ya saka mishi da alheri.
Akwai kuma yaran da suka gama karatu amma babu aikin yi. To su muna da ’yan uwa irin su Jalalu Arabi da Alhaji Umaru Sani, wad'anda su ke 'ko'karin taimakawa wajen sama masu aiki. Ta 'bangaren sana’o’i kuma muna da burin taimakawa; a hankali muna nan muna tunanin yadda duk jama’ar unguwa har ma da matan aure, za su amfana.
Sannan akwai wasu yara masu shaye-shaye, da ’yan sara-suka. Su kuma mun je mun samu Hukumar Ya'ki Da Mu’amala Da Miyagun 'Kwayoyi, NDLEA, da DPO na ’yan sanda don su ba mu gudmmawa don mu tabbatar mun kawar da wad'annan abubuwa daga wannan unguwa tamu. Yanzu haka ma shirin da mu ke yi za mu je mu gana da kwamishinan ’yan sanda don mu had'a kai mu tabbata al’umma ta zauna lafiya. Kuma muna 'ko'karin ganin idan rashin fahimta ya faru a unguwa tsakanin mutum da mutum, to kar a yi saurin zuwa wajen hukuma: a kawo wajen wannan 'kungiya in Allah Ya yarda za ta tabbatar ta sulhunta. Wad'annan kad'an ke nan daga cikin nasarorin da mu ka samu.
Aminiya: Babu shakka ana bu'katar kud'i don gudanar da dukkan wad'annan abubuwa da ka fad'a. Wad'anne hanyoyi wannan 'kungiya ta ke bi don samun kud'in da ta ke gudanar da ayyukan ta?
Alhaji Lawan: A yanzu dai 'kungiya ta na samun kud'in ta ne a tsakanin ’yan 'kungiya. Da farko, mun sanya cewa ko wanne mamba zai bayar da a'kalla naira 50 ko wanne wata. A cikin mu kuma, akwai wad'anda Allah Ya fifita su, wad'anda in wani abu ya taso za mu je wajen su, su cire abin da ke aljihun su a cikin arzi'kin da Allah Ya ba su su ce a je a yi.
Wannan abu da mu ke ta yi duka a jikin mu ne. Mu ya mu ne mu ke ta 'ko'karin samo wannan kud'i. Lokacin da muka fara wannan al’amari, mun fara ne da neman taimakon motar d'aukan gawa. To a wancan lokacin mun samu kud'i isassu, mun sayi wannan mota tana nan tana aiki. To kud'in da suka saura a wancan lokacin su ne su ka zama tsanin da muka taka mu ka fara yin wad'annan ayyuka.
Wad'annan ’yan hanyoyi su ne 'kungiyar nan ta ke bi a yanzu ta ke samun kud'i, amma nan gaba za ta fad'ad'a su in Allah Ya yarda.
Aminiya: Akwai wani taimako ne da ku ke samu daga gwamnati da kuma sauran jama’ar gari?
Alhaji Lawan: Ba mu fara tuntu'bar gwamnati ba tukuna; domin da muka fara 'kungiyar ba ta da kundin tsarin mulki (constitution), sai daga bayan nan muka samu. Yanzu muna 'ko'karin samun rajista ne a hukumar rajistar kamfanoni (CAC). Idan muka samo wannan rajista to mun samu sanda da za mu je gaban gwamnati mu nuna mata 'kungiyar ta kafu ta zauna da gindin ta. In Allah Ya yarda muna kan wannan.
Aminiya: A 'karshe wanne irin kira za ka yi ga al’ummar unguwa don su bayar da had'in kai ga wannan 'kungiya?
Alhaji Lawan: Ina kira ga al’ummar unguwa gaba d'aya su juyo hankalin su su ba wannan 'kungiya had'in kai. Wannan 'kungiya wacce idan suka dube ta da kyau za su ga cewa a duk garin nan ko Jihar nan, babu 'kungiyar da ta ke da manufa da niyya mai kyau kamar ta. Kuma 'kungiyar ta taso a d'an 'kan'kanin lokaci, ta ci nasarori da daman gaske. Saboda haka ina kira ga dukkan al’ummar wannan unguwa su ba wannan 'kungiya goyon baya; duk lokacin da ta kira su su amsa, duk lokacin da ta nemi gudummawar su ko wacce iri ce su bayar. Ba ma mutanen unguwa kawai ba; ina kira ga mutanen gari ne gaba d'aya. Yanzu misali mu na wa garin mu addu’a da ’ya’yayen mu, da kuma addu’ar zaman lafiya. Duk 'karshen wata mu kan taru a d'aya daga cikin masallatan unguwar mu, mu sauke Al-'Kur’ani, mu yi sadaka, mu yi addu’o’i Allah Ya zaunar da mu lafiya: Allah Ya zaunar da garin mu, da Jihar mu, da 'kasar mu lafiya. Kuma ’ya’yayen mu Allah Ya shiryar da su Ya ba su ilimi mai albarka.
Jaridar Aminiya, 11 ga Jumada Ula, 1429 (16 ga Mayu, 2008)

Tuesday, May 06, 2008

Gargad'i Ga Mata

Daga Muhammad K. Muhammad
Sharhin littafin Mu Yi Hattara Mata wanda Maryam Tsoho Mai Doya ta rubuta; Yawan Shafuka: 78; Shekarar wallafa: 2007
Sakamakon wasu rubuce-rubuce da masana irin su Rabaran Thomas Malthus suka yi, wad'anda ke nuna cewa 'karuwar al’umma ya zarta abin da albarkatun da ke duniya za su iya d'auka, 'kasashen Yammacin duniya suka cusa a'kidar rage yawan haihuwa ko ma gudun ta gaba d'aya a zukatan al’ummar su. Irin wannan a'kida ita ce ta yad'u har zuwa 'kasashen Musulmi, inda aka samu wasu, musamman ’yan boko, suka ara suka yafa, duk kuwa da cewa wannan tunani ya sa'ba da karantarwar Musulunci.
A 'ko'karin su na rage haihuwa ko ma guje mata kacokan, wad'annan mutane su kan tilasta matan su na aure shan magungunan hana daukar ciki; idan magungunan ba su yi nasara ba kuma, su kai su a zubar da abin da aka samu. Dalilan su kuwa ba sa wuce tsoron talauci, ko gudun d'aukar nauyi (a ganinsu) da son more rayuwa. Wannan al’amari shi ne ya tayar da hankalin Maryam Tsoho Mai Doya, ta yanke shawarar ta rubuta littafi don gargad'in mata da kuma yin tir da halayen maza masu aikata wannan aika-aika.
Tun tashin farko marubuciyar ta yi shimfid'a da bayar da labarin abin takaicin da ya dame ta har ya kai ta ga tunanin rubuta wannan littafin. A nan ne kuma mallamar ta shaida wa mai karatu cewa idan ana maganar illar matakan hana d'aukar ciki wad'anda Turawa suka kawo, to ita ganau ce ba jiyau ba. Don kuwa ba don ta je asibiti don neman maganin illar da robar hana d'aukar ciki ta yi mata ba, to da ba ta had'u da wata baiwar Allah da ta ba ta tausayi ba.
Mallama Maryam ta had'u da wannan baiwar Allah ne a yayin da ta ke bin layin ganin likita. Ita wannan mata tana ta ajiyar zuciya, lokaci zuwa lokaci kuma tana fad'in “wannan masifa da me ta yi kama?” Daga bisani wannan baiwar Allah ta shaida wa marubuciyar cewa mijin ta baya son haihuwa; don haka sanda ta d'auki ciki ya nemi ta je a zubar da shi, amma da ta 'ki sai ya kamata da duka a cikin har sai da ta suma.
Mu Yi Hattara Mata ya dubi wannan matsala a addinance, sannan kuma ya dube ta a al’adance. Ko wanne daga cikin babi shida na littafin ya fara ne da ayar Al-'Kur’ani ko Hadisin Manzon Allah (SAW). Sannan ya yi nuni da cewa ko a hankali ma, wad'annan abubuwa ne da yawancin al’ummu ba su yarda da su ba, don kuwa kundin tsarin mulki a 'kasashe da yawa ya haramta zubar da ciki. A cewar ta saboda “irin munin da illar wannan d'anyen aiki ke jawowa rayuwar mace, kundin tsarin hukunta laifuffuka na 'kasa, wato Penal Code, a sashe na 232(89) ya tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda ya zubar da cikin wata mace da ganagan, ba da wani dalili na ceton rai ba”.
Littafin ya kuma yi tsokaci game da illolin zubar da ciki wad'anda suka had'a da hujewar mahaifa, da hujewar mara, da kuma zubar jini. Mallamar ta kuma bayyana cewa idan aka samu kuskure wajen cire ciki ba a fitar da dukkan gudajin jinin da ke cikin ba, to wani cikin na iya tashi. Idan ma rashin sa’ar ya 'kara 'kamari, cikin ya kan tashi ne a wajen mahaifa.
Marubuciyar ta kafa hujja da Hadisin da ya ke cewa halittar d'an-Adam a cikin mahaifa na canjawa duk bayan kwana arba’in, da kuma bayanin masana kimiyya a kan halin da d'an tayi ya ke ciki a watanni taran da ya ke ciki, ta jaddada cewa duk wanda ya zubar da ciki bayan kwanaki 120 ya yi kisan kai, ya tozarta rai wanda Allah Ya ba shi ri'kon amana.
Don haka marubuciyar ta ke ganin cewa idan har ba a bu'katar cikin tun farko, bai kamata a yi gangancin d'aukar sa ba. A nan ne kuma ta yi dogon sharhi game da illolin hanyoyin hana d'aukar ciki da Turawa su ka kawo. Kamar yadda ta fad'a a farkon littafin, ta yi amfani da hanyar robar mahaifa wadda a kan sanya a mahaifa (IUCD); amma robar ta haifar mata da tsananin ciwon ciki da ya kai sai da aka yi mata aiki aka cire appendix. Sai dai wannan aiki bai magance ciwon cikin ba: bayan 'karin bincike wata likita ta zayyana wa marubuciyar illolin amfani da wannan roba wadda ta haifar mata da ciwon 'koda.
Marubuciyar ta kuma yi bayanin yadda 'kwayoyin had'iya ke toshe mahaifar mace su kuma samar mata da ciki “na gaibu” wanda a 'karshe ya kan jawo ciwon hanta da rashin sha’awa—wanda shi kuma ya ke haifar da matsala a tsakanin ma’aurata. Haka ma ta yi bayanin sauran hanyoyin hana d'aukar ciki da illolin ko wanne.
Amma marubuciyar ta kawo dalilan da za su iya halatta hana d'aukar ciki ko kawar da shi. Sai dai ta bu'kaci maza da a ko yaushe su tuntu'bi matan su kafin yanke shawarar abin da ya kamata su yi, don kuwa, a cewar ta, matan nan abokan zaman su ne ba bayi ba. Sannan ta kawo hanyoyi na al’ada wad'anda Shari’a ta yarda da su don hana d'aukar ciki wad'anda ba su da illa kamar azlu, shayarwa, hawa sama, da sauransu.
Yayin da marubuciyar ta ke kakkausan suka ga maza masu gudun haihuwa, ta yi sassauci matu'ka ga mata masu irin wannan ra’ayi, da ma wad'anda ke gudun haihuwa don tunanin za ta sanya masu saurin tsufa. Sai dai kuma za a iya tsammanin gargad'in da Mu Yi Hattara Mata ya yi a kan illar amfani da muggan hanyoyin hana d'aukar ciki da illolin zubar da shi zai zama hannunka mai sanda a gare su.
Jaridar Aminiya

Wednesday, April 23, 2008

Birnin K’udus: Mallakin Yahudawa ko Musulmi?

Sunan Littafi: 'Kudus Birni Ne Na Musulunci
Marubuci: Nuruddeen Ibrahim Kano da Ustaz Abu Hanifa Jibreel Assalafi.
Mai Sharhi: Bashir Yahuza Malumfashi.
Kamfanin Wallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano.
Shekarar Wallafa: 2008.
Yawan Shafuka: 90.
Farashi: Ba a fad'a ba.
Kowace a'kida kake bi, kowane addini kake bi, idan dai saukakku ne daga Allah a tarihance, to birnin 'Kudus abin ala'kantawarka ne. Wannan kuwa haka yake a tarihance, domin kuwa muhimman, bun'kasassun, ingantattun addinan nan uku da suka shahara kuma suka bun'kasa a duniya, suna da muhimmin tasiri da tarihi da ala'ka da birnin 'Kudus. Wad'annan addinai kuwa kamar yadda muka sani, su ne Yahudanci, Kiristanci da kuma Musulunci. Dalili ke nan wad'annan mawallafa suka gudanar da ingantaccen bincike, suka rubuta wannan littafi da muke sharhi a yau. Kuma babu shakka ba su yi 'kasa a gwiwa ba, domin kuwa sun tabbatar kuma sun gabatar da gamsassun hujjoji da bayani da suka nuna cewa, lallai 'Kudus birni ne na Musulunci.
Hujja kyakkyawa kuma mai gamsarwa da za ta 'kara tabbatar da jigo da i'kirarin wannan littafi ita ce, dukkan Annabawan da Allah (SWT) Ya aiko a bayan 'kasa Musulmai ne, balle kuma Manzannin da suka zo da muhimman littattafan Attaura (Musa, Alaihis Salam), Injila (Isa, Ruhullah) da Al'kur’ani (Muhammadu, Sallallahu Alaihi Wasallam), dukkansu suna da ala'ka da wannan muhimmin birni na 'Kudus.
Idan muka yi nin'kaya cikin littafin nan, da farko dai za mu iya cewa an yi masa aikin wallafa mai inganci, musamman ta fuskar d'ab’insa, wanda aka yi da haruffa masu girma, ta yadda kowa zai iya karanta shi cikin sau'ki. Na biyu, an yi amfani da takarda mai inganci, wadda ta sha bamban da wadda wasu mawallafa ke amfani da ita mai araha, wacce ba ta dace da buga littafi mai muhimmanci ba. Na uku kuma, an yi aiki mai yawa, ta yadda aka tsarkake littafin daga manyan kura-kuran d'ab’i da suka zama ruwan dare a mayawaitan littattafan Hausa. Na hud'u, an yi amfani da salo da sigar wallafa ta zamani, ta yadda aka bi 'ka’idojin wallafa kamar yadda ake bu'kata; wannan kuwa ya had'a da samar wa littafin Lambar Littafi Ta Duniya. Yin haka ma ya 'kara bambanta littafin daga mafi yawan kwashi-kwaraf d'in littattafan da wasu marubuta ke wallafawa ta hanyar yin wallafar tuwona-maina, ko kuma mu ce dakan-d'aka-shi'kar-d'aka-tankad'en-bakin-gado.
Littafin dai yana 'kunshe da gabatarwa har kala uku daga shafi na biyar zuwa na goma. Wannan kuwa sun had'a da gabatarwar kamfanin wallafa da gabatarwar marubuci na farko da kuma gabatarwar marubuci na biyu, wanda ya kasance mai fassara.
Daga shafi na goma sha d'aya zuwa na sha hud'u kuwa, an yi bayani ne game da abin da marubutan suka kira, Mashigar Maudu’i, inda nan suka yi ta'kaitaccen bayani game da ita kanta daular Falasd'inu, inda nan birnin 'Kudus yake da kuma sauran muhimman garuruwan da ke cikin yankin. Bayanin kuma ya had'a har da kawo taswirar 'kasar Falasd'inu, wadda ke d'auke da sunayen garuruwan 'kasar gaba d'aya.
Daga shafi na goma sha biyar zuwa na ashirin da d'aya kuwa, ya kasance Fasali Na Farko, inda aka yi bayani game da tarihin kafuwar birnin 'Kudus. Haka kuma an yi dogon bayani game da fad'in birnin da yanayinsa; inda a ciki aka zayyana cewa birnin na d'auke ne da 'kofofi har guda bakwai, wad'anda suka had'a da 'kofar Amuud, 'kofar Saahirah, 'kofar Magaaribah, 'kofar Annabi Dawud, 'kofar Khalil da kuma Sabuwar 'Kofa. Haka kuma, an kawo tarihin tsofaffin mazauna birnin na 'Kudus, inda aka tabbatar da cewa al’ummomi biyu ne asalin mazauna birnin, wad'anda suka kasance al’ummar Kan’ana da ke zaune a tsakiyar Falasd'inu da kuma Falasd'inawa da ke zaune a gefen ruwa daga shiyyar kudu.
Daga shafi na ashirin da biyu zuwa na arba’in da biyu na littafin kuwa, nan mai karatu zai tsinkayi Fasali Na Biyu, inda aka yi bayani dalla-dalla game da matsayin birnin 'Kudus a addinance. An fayyace falalar 'Kudus, kamar yadda Al'kur’ani ya bayyana a cikin wasu ayyanannun ayoyi. Haka kuma, an kawo falalar birnin 'Kudus a cikin Sunnah tsarkakakkiya, inda kuma marubutan suka kawo wasu ingantattun Hadisan Manzon Allah (SAW), inda ya yi magana game da falalar birnin ga Musulmai da Musulunci. Sun kawo tarihin yadda aka yi har Annabi Ibrahim (AS) ya yi hijira zuwa birnin na 'Kudus, inda tarihin ya nuna cewa ya yi wannan hijira ne da shekaru dubu biyu kafin haihuwar Annabi Isa (AS). A nan ne kuma marubutan suka kawo hujjar da ta tabbatar da cewa lallai Annabi Ibrahim (AS) ba Bayahude ba ne kamar yadda Allah (SWT) Ya tabbatar a cikin Al'kur’ani mai girma (Al-Imran, 67-68).
Duk dai a cikin wannan fasali na biyu na littafin, an kawo bayanin wasu wurare masu tsarki na Musulunci a birnin 'Kudus. Wad'annan kuwa sun kasance Masallacin 'Kudus, Hubbaren Sakhara da kuma Masallacin Sayyidina Umar (RA). Marubutan sun yi 'ko'karin buga hotunan Masallacin na 'Kudus da kuma Hubbaren Sakhara a shafi na talatin da biyar na littafin, kuma hotunan duk suna cikin kala.
Wannan fasali na biyu bai kammala ba sai da marubutan suka kawo tarihi game da ’ya’yan Isra’ila, wato Annabi Ya'kuba (AS) ke nan. Sun kuwa kawo gamsassun bayanai tare da ayoyin Al'kur’ani da suka kafa hujja da su. Babu shakka, hakan da suka yi ya 'kara wa tarihin inganci, wanda zai gamsar da masu bincike; wanda haka kuma zai kauce wa shakku.
Abu ne sananne cewa, babu yankin da ya sha gwagwamayar ya'ki da tashin hankali, kuma yake cikin kan ganin ya'ke-ya'ke har yau d'in nan, kamar yankin 'Kudus, wanda haka ya sanya babu yadda za a yi tarihin yankin ya kammala ba tare da kawo bayanan ya'ko'kin da suka faru a yankin ba. Babu mamaki da marubutan littafin suka ware Fasali Na Uku na littafin, wanda ya faro tun daga shafi na arba’in da uku har zuwa shafi na saba’in da d'aya, inda nan ne aka ba da tarihin yadda aka ci garin 'Kudus da ya'ki, sannan kuma aka bayyana dukkan ya'ko'kin da aka gwabza a cikinsa.
An yi bayani game da yadda aka bud'e birnin 'Kudus ta hannun Umar 'Dan Khad'd'ab (RA), wanda shi ne ya zama Khalifa bayan rasuwar Khalifa Abubakar (RA). Daga nan kuma sai bayanin Ya'kin Kuros, wanda Turawa suka assasa wa 'Kudus. Nan ma an yi bayani dalla-dalla, aka bayyana duk yadda ta kwaranye. Daga nan kuma sai suka kawo tarihin yadda aka bud'e 'Kudus ta hannun bawan Allah, Salahuddin Ayyubi.
Daga shafi na saba’in da biyu zuwa shafi na tamanin da takwas kuwa, nan aka kawo Fasali Na Hud'u kuma na 'karshe a littafin. Nan ne kuma aka kawo halin da birnin 'Kudus yake ciki a yau. A ciki ne aka yi bayanin yadda aka yahudantar da birnin na 'Kudus, wanda haka ya faru bisa makircin da Yahudawan duniya na zamani suka yi had'in baki, suka mallake yankin a yau. Haka kuma, an kawo bayani da tarihin yadda aka Kiristantar da birnin na 'Kudus. Sannan kuma daga 'karshe aka kawo tarihin dalili da kuma abin da ya sanya Musulmi suka 'kaurace wa birnin 'Kudus, duk kuwa da cewa su ne suka fi cancanta da mallakarsa.
Daga shafi na tamanin da bakwai kuwa zuwa na casa’in, an kawo marufin da ya rufe littafin, inda kuma aka kawo jerin gwanon sunayen littattafan da marubutan suka gudanar da bincike da nazarinsu don rubuta wannan littafi.
Kamar yadda muka gabatar a baya, babu shakka samar da wannan mashahurin littafin a yau, zai tada tsimin Musulmi domin su gane muhimmancin birnin 'Kudus a gare su, sannan su yi ho'b'basan kawo d'auki na yadda za su sake mallakar abinsu, wanda magabatan 'kwarai sun dad'e da yin kira ga haka. Haka kuma littafin ya yi 'ko'karin daidaita tarihi na gaskiya, inda suka wanke kuma suka wancakalar gur'bataccen tarihin da Yahudawa da ’yan kanzaginsu suka bayyana game da yankin.
Babu shakka, masana sun sha nanata cewa, hannun marubuci makaho ne, kamar kuma yadda suka tabbatar da cewa littafi d'aya ne a duk duniya da babu kure a cikinsa, wanda ya kasance Al'kur’ani mai girma. Don haka, bayan na kammala karanta littafin nan, duk da cewa an yi 'ko'kari sosai wajen kauce wa bayyanar kura-kurai, to amma da 'kyar da ji'bin goshi idanuwana suka kallo wasu daga abin da nake ganin cikashi ne ga littafin, duk da cewa ba su taka kara sun karya ba.
Abu na farko shi ne, hoton bangon littafin. A gani na, maimakon hoton Hubbaren Sakhara da aka sanya a bangon littafin, ya kamata a ce hoton Masallacin 'Kudus aka sanya. Domin kuwa, a can baya, an samu Yahudawa suna yad'a hoton hubbaren a matsayin Masallacin 'Kudus, wanda haka ya sanya wasu Musulmin suka d'auka kamar hubbaren ne ma masallacin. Da an yi amfani da hoton Masallacin, da ya fi tasiri wajen daidaita tunanin wasu da suka zaci hubbaren ne masallacin.
Kuskure na biyu da na ci karo da shi a littafin shi ne, yadda aka yi ta amfani da 'kananan ba'ka'ke wajen rubuta kalmomin musulmi da musulunci a dukkan shafukan littafin. Ya dace a ce an yi amfani da manyan ba'ka'ke kamar haka: Musulmi, Musulunci, domin kaurara muhimmancin sunayen.
Haka kuma, a shafi na 35, an samu kuskuren rubuta sunan Masallacin 'Kudus, inda harafin ('K) ya kasance ba a canza shi zuwa harafin Dokta Abdallah ba.
A shafi na 89 zuwa na 90 kuwa, inda aka kawo sunayen littattafan da aka duba, an kawo su ne da haruffan Larabci, maimakon a kawo su da haruffan Hausa, tunda da harshen Hausa ne aka fassara littafin.
Duk da wad'annan ’yan kura-kurai da suka bayyana a littafin, babu shakka dole a jinjina wa 'ko'karin marubutan nan, domin kuwa sun jaddada kuma sun tsarkake tarihi, wanda ba 'karamin makami ba ne na farfaganda da Yahudawa suka dad'e suna amfani da shi wajen cutar da Musulunci da Musulmi.

Wassalam.
Bashir Yahuza Malumfashi
Aminiya, Abuja.

Monday, March 24, 2008

'Yar'aduwa A Taron OIC: Ihu Bayan Hari

Duk mai lura da al’amuran yau da kullum ya san cewa Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (Christian Association of Nigeria [CAN]) a koyaushe tana nuna 'kiyayyarta a fili ga duk wani abu da ya shafi Musulmi ko Musulunci, ko da kuwa wannan abin yana da amfani ga al’umma. Don haka ba abin mamaki ba ne idan 'Kungiyar ta yi suka ga halartar Malam Umaru ’Yar’aduwa taron 'kasashen Musulmi da aka yi a Senegal. Abin mamaki, a gani na, shi ne da ’Yar’aduwa ya ma halarci taron.
A watan Janairun wannan shekara, Sakatare-Janar na 'Kungiyar 'Kasashen Musulmi (Organisation of Islamic Conference [OIC]), Farfesa Ekmeleddin Ihsanoglu, ya kawo ziyara Nijeriya. Kafin ya zo 'kasar kuwa sai da ya biya ta wasu 'kasashen Afirka.
Kamar yadda manema labarai suka ruwaito, Ihsanoglu ya zo Nijeriya ne don ganawa da jami'an gwamnati, da Sarkin Kano, da kuma Sarkin Musulmi dangane da rawar da OIC za ta taka wajen kawar da talauci da cututtuka a Nijeriya. Amma abin ba'kin ciki, haka wannan babban ba'ko, wanda ya taho da kyakkyawan nufi, ya koma ba tare da ya samu ganin wad'annan jami'ai ba.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, yayin da Sarkin Kano ba ya 'kasar lokacin da jami'in OIC d'in ya zo, Fadar Sarkin ta bayyana cewa ba su da labarin zuwan Ihsanoglu. Makamancin wannan bayani ne ya fito daga Fadar Sarkin Musulmi a Sakkwato. Sai dai shi Ihsanoglu ya tabbatar da cewa tun kafin ya taso daga Hedikwatar OIC, jami'an ofishin jakadanci na 'kasarsa, Turkiyya, sun tabbatar masa sun tuntu'bi jami'an Nijeriya wad'anda suka tabbatar masu cewa komai ya kammala don kar'bar wannan babban ba'ko.
Amma abin takaici, sai ga shi yayin da a sauran 'kasashen da ya ziyarta Ministocin Harkokin Waje ke tarbar Sakataren na OIC, sannan daga bisani ya gana da Shugabannin wad'ancan 'kasashe. Amma a Nijeriya, sai wani permanent sakatare a Ma'aikatar Harkokin Waje aka tura ya taro Ihsanoglu. Duk da cewa Ministan Harkokin Waje ba Musulmi ba ne, to ya kamata a ce ya tura d'aya daga cikin 'Kananan Ministocinsa (wanda Musulmi ne). Amma da ya ke ba su d'auki Ihsanoglu da muhimmanci ba ba a yi hakan ba.
Ba kuma za mu manta da cewa bayan Ihsanoglu ya bar 'kasar nan ba tare da ganin 'Yar'aduwa ba, jami'an kamfanin Siemens, kamfanin da aka zarga da bayar da ma'kudan kud'ad'e cin hanci ga wasu manyan jami'an Nijeriya sun kawo ziyara, kuma 'Yar'aduwa ya tarbe su a Aso Rock Villa, yana mai annashuwa da sakin fuska. Wannan ya nuna cewa wula'kancin da aka yiwa Ihsanoglu da gangan aka yi; saboda shi ba d'an jari-hujjan Yammacin duniya ba ne.
Don haka na ke ganin wad'anda ke jan akalar Gwamnatin 'Yar'aduwa - wata'kila - ba da son ransu ya halarci taron OIC ba. Babu mamaki sune suka zugo CAN ta fad'i abin da ta fad'a duk da cewa surutai ne kawai marasa tushe bare makama.

Saturday, March 15, 2008

Jakin Dawa Ya Ga Na Gida

Allah wadaran naka ya lalace, wai jakin dawa ya ga na gida.

Ya zuwa yanzu dai ya kamata a ce mugun 'bacin ran da hukuncin Kotun Saurarar 'Karar Za'ben Shugaban 'Kasa da aka a watan Afrilun bara ta yanke ya fara yayewa. Amma ba'kin cikin da wannan al'amari ya haifar abu ne wanda za a dad'e yana zogi a zukatan mafi yawan 'yan Nijeriya.
Kowa dai ya ji yadda wannan kotu, babu kunya bare tsoron Allah ta yi fata-fata da dukkan hujjojin da aka gabatar a gabanta, alhali kuma, kamar yadda lauyan Janar Muhammadu Buhari ya zayyana, ta ma hana a gabatar da wasu shaidun 'kwarara. Abin da ya fi komai 'kuna shi ne yadda wannan kotu ta wanke Shugaban Hukumar Za'be, Maurice Iwu daga duk wani laifi, alhalin ko shi kansa Malam Umaru ya fad'a da bakinsa cewa an tafka aika-aika a wannan za'be.
To dama dai mutane da yawa sun ce "a rina" (wai an saci zanin mahaukaciya) lokacin da labari ya bayyana cewa Malam Umaru ya gabatar da sunan shugaban wannan kotu a gaban Majlisar Dattijai don a masa 'karin girma zuwa Koyun 'Koli ta 'Kasa. Wasu sun nuna cewa wannan al'amari tsautsayi ne don kuwa ba Malam Umaru ba ne ya za'bo Ogebe. Amma abin da wa'kila mutane ba su yi la'kari da shi ba shine al'amarin nan fa a wajen PDP na ko-a-mutu-ko-a-yi-rai ne. Me zai hana PDP ta yi amfani da wasu mutane a Hukumar Kula da Harkokin Shari'a ta 'Kasa (National Judicial Commission [NJC]) wajen ganin an mi'ka wad'annan sunaye a daidai lokacin da ya dace?
A halin da ake ciki yanzu dai, Majalisar Dattawa ta tabbatar da cicci'ba Ogebe zuwa Kotun 'Koli. Sai dai rahotanni suna nuna cewa lokacin da aka zo mi'ka sunayen mutum biyu don cike gurbin da ke Kotun 'Kolin akwai wani jajin da shi ma ya cancanci tafiya amma ya janye don baiwa Ogebe dama. Haka zalika rahotanni na dad'a nuna cewa lokacin da ake muhawara a Majalisar Sanatoci, wani Sanata ya nuna cewa idan aka bi 'ka'idar cika gurabu bai kamata Ogebe ya je Kotun 'Koli ba saboda tuni Jihar da ya fito, wato Binuwai, tana da wakilcin Mai Shari'a Katsina-Alu, amma sanatocin suka yi watsi da wannan mulahaza.
Wasu rad'e-rad'i da ke kewayawa a Abuja bayan yanke wancan hukunci na cewa da farko ba duka alkalan kotun ne ma suka goyi bayan wancan d'anyen hukuncin ba. A cewar wad'annan rad'e-rad'e ta hanyar matar d'aya daga cikin al'kalan aka bi aka sauya masa ra'ayi.
Idan dai aka je aka zo, ko ma dai yaya aka yi, wannan hukunci da Ogebe ya jagoranci yankewa ya tabbatar da abu d'aya: duk magud'in za'ben da za a tafka a 'kasar nan, komai muninsa, ba laifi ba ne a dokar 'kasa. Don haka a gaba kowa sai ya zage, ya zage damtse ya tafka iyaka iyawarsa: duk wanda ya ci ya sha wanda ya tsaya gaskiya kuwa, to sai dai ya yi Allah Ya isa. Ba shakka kuwa Allah isashshe ne, kuma idan ba ba ji kunya a duniya ba, to tabbas za a ji ta a Lahira.

Monday, February 04, 2008

Albasa (Ba) Ta Yi Halin Ruwa (Ba)


Masu iya magana ne ke cewa “Albasa ba ta yi halin ruwa ba” idan aka samu wani mutum ya sa'ba d'abi’ar da ake zaton gani a wurinsa ko wurinta (wanda ya kamata a ce ta/ya gada). Idan kuwa albasar ta yi halin ruwa, sai ka ji sun ce “Barewa ba ta gudu d'anta ya yi rarrafe”.
Wata'kila idan mutum ya dubi hoton da ke saman wannan ma'kala (idan shugaban 'kasa Malam Umaru 'Yar'aduwa ke gabatar da 'yarsa ta cikinsa [ta gefen hagu] ga Sakatariyar Harkokin Waje ta Amurka, Condoleezza Rice) ya yi tambaya: “Shin albasa ta yi halin ruwa, ko ba ta yi ba?” Ha'ki'ka na ga wani marubutci ya yi 'ko'karin yin wannan tambaya ko da ya ke bai bayar da amsa ba.
Lokacin da uwar gidan Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Zainab Shekarau, ta kai ziyara Katsina don taya iyalan Malam Umaru Musa 'Yar’aduwa murnar cin za'ben shugaban 'kasa da ya yi, ta bayyana cewa ala'kar su da nata iyalin ba a fagen siyasa ta samo asali ba. A cewar ta sun sha had'uwa da uwar gidan Malam Umaru a wuraren da'awa. Ma’ana su kan had'u a wuraren da a kan yi kira don shiryar da jama’a zuwa ga karantarwa irin ta addinin Musulunci!
A nan idan muka kwatanta irin shigar da mukan ga Hajiya Turai ta yi a hotunan jaridu da talabijin da irin suturar da Musulunci ya karantar da mata su sanya, ma iya cewa uwar gidan Shugaban 'Kasar ba ta aiki da abin da ta ke fadi? Wata'kila ma iya cewa ai uwar gidan Shugaban na suturta jikinta, illa wani 'bangare na wuyanta da ya kan fito jifa-jifa (wata'kila don a ga irin gwal d'in da ta sanya mai tsada), don haka tana aikata abin da ta ke fad'i.
Idan haka ne, ya zamu yi da maganar da a kan ce wai “sai gida ya 'koshi a kan bai wa waje”, ko kuma “tarbiyya daga gida ake faro ta”? Ya aka yi Hajiya Turai ta yi ta yawon da’awa don shiryar da wad'ansu amma ta kasa shiryar da 'ya'yanta? Don kuwa ba yarinyar da muke gani a wannan hoto na sama ce kad'ai ta ta'ba shiga mai ayar tambaya ba. Kwanan baya mutane da yawa sun yi ta surutu a kan irin tufafin da d'aya 'yar tata wadda ta auri wani gwamna ta sanya lokacin auren nata.
Amma fa kar mu manta cewa uba shi ake tsammani zai yi tsayin daka don tarbiyyantar da 'ya'yansa. To mai ya hana Malam Umaru yi wa 'ya'yansa tarbiyya musamman ta 'bangaren irin tufafin da ya dace su sanya?
A nan yana da kyau mu tuna cewa idan ana ambatar labarin rayuwar Malam Umaru a kance lokacin yana ala’kanta kansa da 'bangarancin siyasa da a turance ake kira left (wato hagu). Sannan kuma ana nuna cewa Marigayi Dokta Bala Usman (lokacin yana tashen ra’ayi irin na gurguzu) ya yi tasiri matu'ka a kan Malam Umaru. A sanin kowa ne kuma cewa zai yi wuya ka samu mai ra’ayin gurguzu da ba ya ra’ayin Makisanci (Marxism).
To ko dai da shi bai d'au wannan ra’ayi na Makisanci ba, uban da zai 'kyale 'yar sa tana irin wannan shiga to wata'kila irin mutanen nan ne da Mallam Muhammad Bin Usman ya kira 'yan boko a'kida*. Ke nan an d'auki boko da muhimmancin da ya sa ake ganin cewa wayewa ta 'kunshi d'abi’u irin na Yahudu ko da kuwa sun sa'ba da al’adun gado.
Amma fa kar mu manta da maganar da Hausawa kan yi: “Ka haifi yaro ba ka haifi halinsa ba”. Ko wannan na iya zama dalili da za mu iya cewa iyaye su na da uzuri idan 'ya'yansu suka fara yin shigar da ba ta dace ba? Hasali ma a iya bayar da misali (musamman ta 'bangaren Hajiya Turai) da Annabi Nuhu da d'ansa.
Ni a gani na wannan ba uzuri ba ne. Don kuwa in har mutum ya tsaya tsayin daka wajen tarbiyyar 'ya'yansa, da addu'ar Allah Ya shirya su, to zai yi wuya a ce dukkansu sun fand'are. Kar mu manta - kamar yadda muka fad'a a baya - wannan yarinya ba ita kad'ai ce kafofin yad'a labarai suka haska mana hotonta da shigar da ba ta dace da mu ba. Ke nan ko dai albasa ta yi halin ruwa (ma’ana barewa ba ta yi gudu d'anta ya yi rarrafe ba) ko kuma mai dokar barci ya 'bige da gyangyad'i.
Abin nufi shine Hajiya Turai ta kasa shiryar da iyalinta (alhali ko Manzon Allah [SAW] kafin a ba shi umarnin kiran kowa da kowa sai da aka fara umartar sa ya kira danginsa na kusa) ta fita shiryar da na waje. Abin tambaya a nan shi ne: “Ta yaya wanda ya kasa jagorancin gidansa zai jagoranci 'kasa irin Nijeriya?
______________________________________
* Mallam Muhammad Bin Usman ya yi bayanin cewa 'yan boko sun kasu uku: (1) 'Yan boko a'kida/addini, (2) 'Yan boko sana'a, da kuma (3)'Yan boko manufa.

Friday, January 25, 2008

Shin Me Jang Yake Nufi da Jos?


Alamu na nuna cewa duk wata gwamnati da ta kafu a Jihar Filato tana zuwa da wasu manufofi na musamman dangane da garin Jos da kuma 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa. Wannan, ko shakka babu, ba zai rasa nasaba da kasancewar wannan wuri cibiyar mulki da hada-hada ta Jihar ba. Amma babu gwamnatin da ta zo da d'amsul basirati, da rashin hangen nesa, da kuma tsananin d'imuwa kamar gwamnatin Jang.
Da farko dai, kasancewa tun bayan kafa Jihar ba a ta'ba samun d'an 'kabilar Birom d'in da aka za'ba don ya mulke ta ba, wannan gwamnati, ga alama, ta zo da burin ganin ta tabbatar da duga-dugan ‘yan 'kabilar Birom a kan madafun iko a Jihar. Kwanan nan wani mai baiwa tsohon gwamna Joshua Dariye shawara ya koka cewa Gwamna Jang ya kori wasu jami’ai ya maye gurbinsu da ‘yan wata 'kabila guda d'aya.
A irin wannan yun'kuri, wata'kila Jang yana so ne ya ga cewa mutanensa sun kame Jos, kamun kazar kuku, domin wannan zai taimaka musu wajen yin yadda suka so da Jihar, duk da cewa ‘yan 'kabilar Birom d'in da ke 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa ba su taka kara sun karya ba. Wannan dalili ne ya sa ya ke so ya fad'ad'a fadar Gbong Gwom Jos, bayan ya tashi Sakatariyar 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa daga inda take. Kamar yadda wata majiya ta ruwaito har ma katafariyar majami’a (coci) wadda babu irinta a 'kasar nan za a gina a wurin.
Abu na biyu kuma shine 'kir'kirar wasu 'kugiyoyin shara da aka yi ba tare da tuntu'bar al'ummar gari ba, aka wakkala musu bi unguwa-unguwa a garin Jos don kwashe shara, a 'karshen mako kuma su kar'bi wasu kud'ad'e daga hannun jama’a. yawancin kwandunan sharar da wad'annan mutane suka ajiye a wuraren kasuwanci ne inda kud'i ke shiga da fita ba 'ka'k'kautawa. To amma bayan ba su kwashe ko da tsinken tsintsiya a wad'annan wurare ba, sai ga masu kwasar shara sun zo kwasar kud'i. Ci-ma-zaune ke nan!
Haka zalika, wannan gwamnati ta 'kir'kiri wani haraji na babu gaira babu dalili wai shi harajin zaman gari (tenancy rate). Amma na ji hatta tsirarun ‘yan 'kabilar Birom d'in da abin ya rutsa da su suna tofin Allah-tsine; ko da yake ba don su aka yi wannan doka ba.
Baya ga wannan, kwatsam sai gwmnatin Jang tace wai za ta hana yin a-ca'ba a cikin garin Jos da kuma 'Bukur! Jin haka ke da wuya mutane suka fara cewa ai wannan ba wani abu bane illa yun'kurin hanawa wasu jama’a sana’ar da za su yi su ci abinci. A 'kiyasin shugaban ‘yan a-ca'ba na Jihar, dubban mutane ne, yawancinsu matasa, za su shiga halin ni-‘ya-su idan hakan ya tabbata.
Ko da ya ke daga baya gwamnatin ta zo da bayanin cewa Kwamishinan Muhalli da Raya Birane na Jihar, wanda shi ne ya yi waccan maganar, ba da yawun gwamnati ya yi ta ba, masu iya magana sun ce wai “idan ka ga kare yana sansana takalmi to d'auka zai yi. Ma’ana, babu wani kwamishina da zai zo ya yi magana ta 'kashin kansa a kafofin yad'a labarai ba tare da ya fayyace cewa wannan magana ra’ayinsa ce ba, sannan kuma ya ci gaba da ri'ke mu'kaminsa.
Da ma can an ta'ba rad'e-rad'in cewa Majalisar Dokoki ta Jihar Filato ta yi yun'kurin hana aca'ba amma ta fasa saboda idan ta yi hakan ‘yan aca'ba da yawa za su koma makaranta. To idan gwamnatin Jang ta yi nasarar hana aca'ba, wasu daga cikin ‘yan aca'ba za su koma makarantu don 'karo ilimi, wasu kuwa makarantun ashsha za su shiga. Ma’ana wad'anda ba za su iya komawa makaranta ba, babu shakka za su shiga sace-sace ne, da aikata sauran laifuffuka. Wata'kila sannan Jang zai yi 'ko'karin magance wannan matsala ta hanyar sanyawa a karkashe su. Don dama manufar it ce a kore su daga garin 'karfi da yaji.
Dukkan yun'kurin da aka yi a baya na ganin an karya wannan al’umma ya 'ki yin tasiri. Baya ga 'kona kasuwar Jos da gangan don ganin an talauta su, an 'ki sake gina ta da gangan. To amma a maimakon su karye, sai 'kara bun'kasa su ke yi, Allah Yana 'kara musu arzi'ki da wadata. Dama Hausawa sun ce, “Wani hanin ga Allah baiwa ne”.
Idan ba a manta ba, lokacin da ya tsaya takara a 'kar'kashin jam’iyyar ANPP a shekarar 2003, Jang ya yi al'kawarin zai sake gina Babbar Kasuwar Jos. Ya yi wannan al'kawarin ne lokacin da ya je ya'kin neman za'be a 'Karamar Hukumar Jos ta Arewa, sanin cewa mafi yawan mutanen da ke da rumfuna a kasuwar mutanen 'Karamar Hukumar ne. Amma yanzu sai ga shi Gwamnan ya nuna cewa ba zai sake gina kasuwar ba, duk da cewa lokacin dokar ta 'baci Kantoman Jihar, Kanar Kiris Alli mai ritaya ya ma bayar da kwangilar sake ginin. A maimakon haka Jang nema ya ke ya tursasa mutane su koma wani fa'ko wanda ya ke nesa da idon jama’a; hala bai ta'ba jin wa'kar Marigayi Alhaji Mamman Shata ba inda ya ke cewa: “Yawan mutane shi ne kasuwa, ni ku raba ni da tarin rumfuna”.
Abin 'karin ban haushi ma shi ne rad'e-rad'in cewa Jang yana nema ya tashi mutanen da ke 'Karamar Kasuwar Jos wadda aka fi sani da suna “New Market”—inda ‘yan kasuwa da d'an dama suka koma suka tsuguna bayan tarwtsa Babbar Kasuwa. A maimakon kasuwar, wai Jang so ya ke yi ya gina dandalin sha'katawa. To Allah Ya sa wannan labari ya 'kare a jita-jita; don in ba haka ba, kusan dukkan abubuwan da Jang ya ke shiryawa za su zama abin da bature ya ke cewa “To cut the nose in order to spite the face”, ma’ana, a garin neman gira za a rasa ido.
Yana da kyau a fahimci cewa tarihi ya nuna babu wata 'kasa ko al’umma da za ta ci gaba ita kad'ai ba tare da cud'anya da mu’amala da wasu wad'anda ta ke ganin bare ne ba. Duk wata wayewa a tarihin duniya sakamakon musayar ra’ayi ne da cud'anya a tsakanin al’ummu daban-daban. Ko ci gaban da a ke ganin Amurka—'kasar da a ke ta han'koron kwaikwayo a wannan zamanin—ta yi, had'uwar al’ummu da dama ne ya kawo shi. Ko a nan Nijeriya ma, garuruwan da suka bun’kasa ta fuskar kasuwanci ko masana’antu, ko ma siyasa, irin su Legas, Kano, da sauransu, za ka samu cewa tare da taimakon al’ummun da suka taso daga wasu wurare suka bun’kasa.