Saturday, March 15, 2008

Jakin Dawa Ya Ga Na Gida

Allah wadaran naka ya lalace, wai jakin dawa ya ga na gida.

Ya zuwa yanzu dai ya kamata a ce mugun 'bacin ran da hukuncin Kotun Saurarar 'Karar Za'ben Shugaban 'Kasa da aka a watan Afrilun bara ta yanke ya fara yayewa. Amma ba'kin cikin da wannan al'amari ya haifar abu ne wanda za a dad'e yana zogi a zukatan mafi yawan 'yan Nijeriya.
Kowa dai ya ji yadda wannan kotu, babu kunya bare tsoron Allah ta yi fata-fata da dukkan hujjojin da aka gabatar a gabanta, alhali kuma, kamar yadda lauyan Janar Muhammadu Buhari ya zayyana, ta ma hana a gabatar da wasu shaidun 'kwarara. Abin da ya fi komai 'kuna shi ne yadda wannan kotu ta wanke Shugaban Hukumar Za'be, Maurice Iwu daga duk wani laifi, alhalin ko shi kansa Malam Umaru ya fad'a da bakinsa cewa an tafka aika-aika a wannan za'be.
To dama dai mutane da yawa sun ce "a rina" (wai an saci zanin mahaukaciya) lokacin da labari ya bayyana cewa Malam Umaru ya gabatar da sunan shugaban wannan kotu a gaban Majlisar Dattijai don a masa 'karin girma zuwa Koyun 'Koli ta 'Kasa. Wasu sun nuna cewa wannan al'amari tsautsayi ne don kuwa ba Malam Umaru ba ne ya za'bo Ogebe. Amma abin da wa'kila mutane ba su yi la'kari da shi ba shine al'amarin nan fa a wajen PDP na ko-a-mutu-ko-a-yi-rai ne. Me zai hana PDP ta yi amfani da wasu mutane a Hukumar Kula da Harkokin Shari'a ta 'Kasa (National Judicial Commission [NJC]) wajen ganin an mi'ka wad'annan sunaye a daidai lokacin da ya dace?
A halin da ake ciki yanzu dai, Majalisar Dattawa ta tabbatar da cicci'ba Ogebe zuwa Kotun 'Koli. Sai dai rahotanni suna nuna cewa lokacin da aka zo mi'ka sunayen mutum biyu don cike gurbin da ke Kotun 'Kolin akwai wani jajin da shi ma ya cancanci tafiya amma ya janye don baiwa Ogebe dama. Haka zalika rahotanni na dad'a nuna cewa lokacin da ake muhawara a Majalisar Sanatoci, wani Sanata ya nuna cewa idan aka bi 'ka'idar cika gurabu bai kamata Ogebe ya je Kotun 'Koli ba saboda tuni Jihar da ya fito, wato Binuwai, tana da wakilcin Mai Shari'a Katsina-Alu, amma sanatocin suka yi watsi da wannan mulahaza.
Wasu rad'e-rad'i da ke kewayawa a Abuja bayan yanke wancan hukunci na cewa da farko ba duka alkalan kotun ne ma suka goyi bayan wancan d'anyen hukuncin ba. A cewar wad'annan rad'e-rad'e ta hanyar matar d'aya daga cikin al'kalan aka bi aka sauya masa ra'ayi.
Idan dai aka je aka zo, ko ma dai yaya aka yi, wannan hukunci da Ogebe ya jagoranci yankewa ya tabbatar da abu d'aya: duk magud'in za'ben da za a tafka a 'kasar nan, komai muninsa, ba laifi ba ne a dokar 'kasa. Don haka a gaba kowa sai ya zage, ya zage damtse ya tafka iyaka iyawarsa: duk wanda ya ci ya sha wanda ya tsaya gaskiya kuwa, to sai dai ya yi Allah Ya isa. Ba shakka kuwa Allah isashshe ne, kuma idan ba ba ji kunya a duniya ba, to tabbas za a ji ta a Lahira.