Tuesday, May 06, 2008

Gargad'i Ga Mata

Daga Muhammad K. Muhammad
Sharhin littafin Mu Yi Hattara Mata wanda Maryam Tsoho Mai Doya ta rubuta; Yawan Shafuka: 78; Shekarar wallafa: 2007
Sakamakon wasu rubuce-rubuce da masana irin su Rabaran Thomas Malthus suka yi, wad'anda ke nuna cewa 'karuwar al’umma ya zarta abin da albarkatun da ke duniya za su iya d'auka, 'kasashen Yammacin duniya suka cusa a'kidar rage yawan haihuwa ko ma gudun ta gaba d'aya a zukatan al’ummar su. Irin wannan a'kida ita ce ta yad'u har zuwa 'kasashen Musulmi, inda aka samu wasu, musamman ’yan boko, suka ara suka yafa, duk kuwa da cewa wannan tunani ya sa'ba da karantarwar Musulunci.
A 'ko'karin su na rage haihuwa ko ma guje mata kacokan, wad'annan mutane su kan tilasta matan su na aure shan magungunan hana daukar ciki; idan magungunan ba su yi nasara ba kuma, su kai su a zubar da abin da aka samu. Dalilan su kuwa ba sa wuce tsoron talauci, ko gudun d'aukar nauyi (a ganinsu) da son more rayuwa. Wannan al’amari shi ne ya tayar da hankalin Maryam Tsoho Mai Doya, ta yanke shawarar ta rubuta littafi don gargad'in mata da kuma yin tir da halayen maza masu aikata wannan aika-aika.
Tun tashin farko marubuciyar ta yi shimfid'a da bayar da labarin abin takaicin da ya dame ta har ya kai ta ga tunanin rubuta wannan littafin. A nan ne kuma mallamar ta shaida wa mai karatu cewa idan ana maganar illar matakan hana d'aukar ciki wad'anda Turawa suka kawo, to ita ganau ce ba jiyau ba. Don kuwa ba don ta je asibiti don neman maganin illar da robar hana d'aukar ciki ta yi mata ba, to da ba ta had'u da wata baiwar Allah da ta ba ta tausayi ba.
Mallama Maryam ta had'u da wannan baiwar Allah ne a yayin da ta ke bin layin ganin likita. Ita wannan mata tana ta ajiyar zuciya, lokaci zuwa lokaci kuma tana fad'in “wannan masifa da me ta yi kama?” Daga bisani wannan baiwar Allah ta shaida wa marubuciyar cewa mijin ta baya son haihuwa; don haka sanda ta d'auki ciki ya nemi ta je a zubar da shi, amma da ta 'ki sai ya kamata da duka a cikin har sai da ta suma.
Mu Yi Hattara Mata ya dubi wannan matsala a addinance, sannan kuma ya dube ta a al’adance. Ko wanne daga cikin babi shida na littafin ya fara ne da ayar Al-'Kur’ani ko Hadisin Manzon Allah (SAW). Sannan ya yi nuni da cewa ko a hankali ma, wad'annan abubuwa ne da yawancin al’ummu ba su yarda da su ba, don kuwa kundin tsarin mulki a 'kasashe da yawa ya haramta zubar da ciki. A cewar ta saboda “irin munin da illar wannan d'anyen aiki ke jawowa rayuwar mace, kundin tsarin hukunta laifuffuka na 'kasa, wato Penal Code, a sashe na 232(89) ya tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda ya zubar da cikin wata mace da ganagan, ba da wani dalili na ceton rai ba”.
Littafin ya kuma yi tsokaci game da illolin zubar da ciki wad'anda suka had'a da hujewar mahaifa, da hujewar mara, da kuma zubar jini. Mallamar ta kuma bayyana cewa idan aka samu kuskure wajen cire ciki ba a fitar da dukkan gudajin jinin da ke cikin ba, to wani cikin na iya tashi. Idan ma rashin sa’ar ya 'kara 'kamari, cikin ya kan tashi ne a wajen mahaifa.
Marubuciyar ta kafa hujja da Hadisin da ya ke cewa halittar d'an-Adam a cikin mahaifa na canjawa duk bayan kwana arba’in, da kuma bayanin masana kimiyya a kan halin da d'an tayi ya ke ciki a watanni taran da ya ke ciki, ta jaddada cewa duk wanda ya zubar da ciki bayan kwanaki 120 ya yi kisan kai, ya tozarta rai wanda Allah Ya ba shi ri'kon amana.
Don haka marubuciyar ta ke ganin cewa idan har ba a bu'katar cikin tun farko, bai kamata a yi gangancin d'aukar sa ba. A nan ne kuma ta yi dogon sharhi game da illolin hanyoyin hana d'aukar ciki da Turawa su ka kawo. Kamar yadda ta fad'a a farkon littafin, ta yi amfani da hanyar robar mahaifa wadda a kan sanya a mahaifa (IUCD); amma robar ta haifar mata da tsananin ciwon ciki da ya kai sai da aka yi mata aiki aka cire appendix. Sai dai wannan aiki bai magance ciwon cikin ba: bayan 'karin bincike wata likita ta zayyana wa marubuciyar illolin amfani da wannan roba wadda ta haifar mata da ciwon 'koda.
Marubuciyar ta kuma yi bayanin yadda 'kwayoyin had'iya ke toshe mahaifar mace su kuma samar mata da ciki “na gaibu” wanda a 'karshe ya kan jawo ciwon hanta da rashin sha’awa—wanda shi kuma ya ke haifar da matsala a tsakanin ma’aurata. Haka ma ta yi bayanin sauran hanyoyin hana d'aukar ciki da illolin ko wanne.
Amma marubuciyar ta kawo dalilan da za su iya halatta hana d'aukar ciki ko kawar da shi. Sai dai ta bu'kaci maza da a ko yaushe su tuntu'bi matan su kafin yanke shawarar abin da ya kamata su yi, don kuwa, a cewar ta, matan nan abokan zaman su ne ba bayi ba. Sannan ta kawo hanyoyi na al’ada wad'anda Shari’a ta yarda da su don hana d'aukar ciki wad'anda ba su da illa kamar azlu, shayarwa, hawa sama, da sauransu.
Yayin da marubuciyar ta ke kakkausan suka ga maza masu gudun haihuwa, ta yi sassauci matu'ka ga mata masu irin wannan ra’ayi, da ma wad'anda ke gudun haihuwa don tunanin za ta sanya masu saurin tsufa. Sai dai kuma za a iya tsammanin gargad'in da Mu Yi Hattara Mata ya yi a kan illar amfani da muggan hanyoyin hana d'aukar ciki da illolin zubar da shi zai zama hannunka mai sanda a gare su.
Jaridar Aminiya