Saturday, March 24, 2007

Ina ne Asalin Jasawa?

Ina ne Asalin Jasawa?

Kalmar Jasawa na iya d'aukar ma'anoni guda biyu. Ma'ana ta farko itace ta fuskar sunan al'umma ko mazauna gari; misali, mutanen Kano ana kiran su Kanawa, na Katsina Katsinawa, na Sakkwato Sakkwatawa, da sauransu. Ke nan Jasawa na nufin mutanen Jos, ba tare da an bambance wasu daga wasu ba.

A ma'ana ta biyu, wadda yawanci ita aka fi fassara kalmar da ita, akan ce Jasawa ta samo asali ne daga kalmomi guda biyu: Jos da Hausawa. Ke nan idan aka ce Jasawa ana nufin Hausawan Jos. Ita ma kanta kalmar Jos an yi sa'bani wajen fassara ta. Wasu sun ce kalmar ta samo asali ne daga harshen Birom, wasu kuma sun ce sunan wani bature ne.

Ala ayyi halin, Hausawan Jos Jasawa ne ta ko wacce siga mutum ya fassara wannan kalma. Masana tarihi sun bayyana cewa Hausawa sun kwaranya zuwa wurin da ake kira Jos ne a matakai biyu, ko uku. Matakin farko shine wad'anda ake kira d'iban gwamna.

Lokacin da Turawa suka gano kuza a yankin Tsaunukan Jos (Jos Plateau), sun nemi ma'aikatan da za su yi aikin ha'kar wannan ma'dani, amma ma'aikata sun yi 'karanci. Don haka Turawa suka bu'kaci sarakunan 'kasashen Hausa su samo masu ma'aikata. 'Ko'karin da sarakunan suka yi na rarrashin jama'ar su su yarda su zo wannan aiki ya ci tura; don haka aka kwaso mutane 'karfi-da-yaji aka kawo su.

Kashi na biyu kuma sune 'yan kasuwa, wad'anda su kan kawo kayan biyan bu'kata ga wad'ancan ma'aikatan. Wad'annan 'yan kasuwa su kan tafi 'kasashen Hausa su sayo kaya kama daga kayan abinci zuwa na bu'katun yau da kullum, sannan su kawo su sayar a 'kasar kuza (Jos). Da tafiya tai tafiya sai wasu daga cikin wad'annan 'yan kasuwa suka zama diloli suka share wuri suka zauna - sun ma sun zama 'yan gari ke nan.

Daga nan kuma sai aka samu wani kashin wanda shima na 'yan kasuwa ne. Sai dai su wad'annan ba zuwa suke yi su sayo kaya su zo su sayar ba. Hasali ma su ba mazauna garin ba ne, su kan zo lokacin rani, idan damina ta fad'i kuma sai su koma wuraren da suka fito don yin noma. Wad'annan ake kira 'yan-ci-rani. To suma da tafiya ta yi tafiya wasu daga cikin su Allah Ya yi masu bud'i, sai suka gina gidaje, suka yi aure, suka hayayyafa.

Amma wannan ba yana nufin cewa Hausawa ba su ta'ba zuwa yankin Tsaunukan Jos kafin zuwan Turawa ba ne. Wannan dai shine bayanin yadda Hausawa masu d'imbin yawa suka kwararo suka zauna a yankin.

Da yawa daga cikin mutanen da suka taho Jos daga 'kasashen Hausa ba su zo da niyyar zama ba. Wata'kila ma wannan ne ya sa gidajen da suka gina a wancan lokaci a wuraren da sansanonin ma'aikata suke ba su cika yalwa ba. Misali idan mutum ya shiga unguwar Gangare ko wasu unguwanni makamantan ta zai ga gidajen du-du-du ba su fi a gina d'aki d'aya da falo a wurin ba - amma kuma akwai d'akunan kwana uku ko fiye da na girki, da na wanka ko magewayi.

Kasancewar wad'annan mutane sun taho da niyyar komawa garuruwansu ko-yau-ko-gobe ya sa wasu daga cikin su ba su d'ebi 'ya'yansu sun kai su garuruwansu na asali ba. Wasu dai sun yi 'ko'kari sun shaidawa 'ya'yan nasu sunayen garuruwansu - da yawa ba su samu damar yin hakan ba saboda wasu dalilai da Allah kad'ai Ya sani. Don haka, Jasawa na zamani da yawa wad'anda sune alumma a mataki na uku ko na hud'u, ba su san garuruwan da iyayensu suka samo asali ba.

Bugu da 'kari, kasancewar al'ummar Hausawa Musulmi ne ya sa duk inda mutum ya je ya zauna yana d'aukar wannan wuri tamkar garinsu. A wurin su 'kasa ta Allah ce mai fad'i, duk inda mutum ya samu kanshi sai kawai ya du'kufa bautar Allah da hidimar kyautatawa bayin Allah.

Wad'annan mutane da suka zo, ko aka d'ebo su aka kawo su, su ne suka sadaukar da rayuwar su da duk abin da suka mallaka don gina wannan wuri da ake kira Jos. Kai hatta d'an ci-ranin da ba ya yin wata biyar a garin ya na bayar da gudummawa gagaruma wajen ciyar da wannan gari gaba ta fuskar tattalin arzi'ki.

No comments: